1636 GMT — Isra'ila na aikata laifukan cin zarafin ƴan'adam a Gaza — Erdogan
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Isra'ila, tare da taimakon Amurka da ƙasashen Turai, tana aikata laifukan cin zalin ƴan'adam a Gaza a kwana 25 din da suka wuce.
Da yake yi wa kafafen watsa labarai jawabi bayan taron majalisar zartarwa a Ankara, Erdogan ya ce Isra'ila ba ta girmama duk wata doka ta ƙasa da ƙasa da kuma darajojin ɗa'adam.
"Muna ci gaba da tattaunawa don tabbatar da cewa an kama masu aikata laifukan yaƙi a Gaza da laifi," ya ce.
"Waɗanda suka sanadin kashe dubban yara a Gaza a yau ba su da wata ƙima a kan duk wani batu da za a tattauna a gobe," Erdogan ya jaddada.
1413 GMT — Aƙalla mutum 100 sun mutu a harin da Isra'ila ta kai sansanin ƴan gudun hijira na Jabalia a Gaza
Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta ce a ƙalla mutum 100 ne suka mutu a wani harin sama da Isra'ila ta kai kan sansanin ƴan gudun hijira na Jabalia da ke yankin na Falasɗinu
A cewar sanarwar da ma'aikatar ta fitar, harin ya kuma lalata wani gini mai hawa shida da ke unguwar.
1223 GMT — Sojojin Isra'ila na ta kutsawa can cikin arewaci da tsakiyar Gaza — ma'aikata
Motocin yaƙin Isra'ila suna ci gaba da kutsa wa can cikin arewaci da kuma tsakiyar Gaza, a cewar Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta yankin.
"Ana ta ganin motocin yaƙin Isra'ila a kan babban titin Salahuddin suna ƙoƙarin shiga yankin yamma," kamar yadda Iyad al Buzm ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Turkiyya Anadlou, yana mai magana a kan titin da ya zagaye illahirin tsawon yankin Gaza.
Ganau sun ce dakarun Isra'ila suna kutsawa ta kan babban titi suna durfafar ɓangaren yamma.
"Dakarun Isra'ila sun kuma shiga zirin daga arewa maso yammacin Gaza," a cewar al Buzm.
"A yanzu ana iya ganin motocin yaƙin a gundumar al Karam da ke arewacin Gaza," ya ƙara da cewa.
0130 GMT — Sojin Isra'ila sun ce sun yi ba-ta-kashi da mayaƙan Hamas a Gaza
Dakarun isra'ila sun yi ba-ta-kashi da mayaƙan Hamas a cikin Gaza, kamar yadda rundunar sojin ƙasar ta fada, a yayin da take ci gaba da kutsawa cikin yankin na Falasɗinu da kai hare-hare ta sama.
"Dakarun Isra'ila sun yi ba-ta-kashi sosai da ƴan ta'addan Hamas a can cikin Zirin Gasa," a cewar sanarwar da rundunar sojin ta fitar, tana mai cewa an kashe gwamman mayaƙan Hamas ɗin a cikin ƴan awannin da suka wuce.
1255 GMT — Injinan samar da lantarki a wasu asibitoci za su tsaya cik a Gaza gobe Laraba
Ma’aikatar Lafiya da ke Gaza ta yi gargadi kan cewa manyan injinan da ke samar da wutar lantarki a wasu manyan asibitoci biyu za su daina aiki gobe Laraba saboda karancin man fetur.
Ma’aikatar ta ce hakan ya faru ne sakamakon hana shiga da fetur a birnin da aka yi wa kawanya.
Tun a baya hukumar ta yi korafi kan cewa Isra’ila ta hana shiga da fetur cikin birnin wanda yana da muhimmanci matuka domin a saka wa injinan samar da wutar lantarki.
1127 GMT — An kashe Falasdinawa 8,525 a Gaza zuwa yanzu
Akalla Falasdinawa 8,525 daga ciki har da yara 3,542 aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai tun daga 7 ga watan Oktoba, kamar yadda ma’aikatar lafiya da ke Gaza ta bayyana a ranar Talata.
Ma’aikatar ta ce an kashe ma’aikatan lafiya 130 sannan akwai asibitoci 15 wadanda suka rufe.
1030 GMT — Yara 940 sun bace a Gaza: UNICEF
Asusun Kula Da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi gargadin cewa akwai akalla yara 940 a Gaza wadanda suka bace babu labarinsu.
Haka kuma asusun ya yi gargadi kan cewa Gaza na neman zama makabarta ga yara kanana a halin yanzu.
Asusun ya ce ana kara samun adadin yaran da ke mutuwa a kullum a Gaza sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa
1000GMT — Jami'an diflomasiyyar Qatar da Amurka sun tattauna kan halin da ake ciki a Gaza
Ministan Harkokin Wajen Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani ya tattauna da takwaransa na Amurka Antony Blinken kan hare-haren da Isra'ila take ci gaba da kai wa a Gaza.
Blinken ya kira Al Thani, wanda kuma shi ne firaiministan, ta wayar tarho inda "suka tattauna kan yadda lamura ke ta'azza a Gaza da kuma bukatar tsagaita wuta nan-take," a cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Qatar ta fitar.
Kazalika sun tattauna kan matakan baya-bayan nan game da sulhu domin sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.
0800 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 15 a harin da ta kai wani gida a tsakiyar Gaza
Aƙalla Falasɗinawa 15 ne suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai wani gida na zuri'ar Abu Shamala a unguwar Zawaida da ke yankin tsakiyar Gaza, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA ya bayyana, yana mai ambato majiyyin watsa labarai.
WAFA ya ce jiragen yaƙi sun kuma kai hari wani gini mai hawa huɗu a unguwar Zaytounda ke kudu maso gabashin Gaza, inda gwamman mutane suka jikkata.
Sojojin Isra'ila na ci gaba da kai hare-haren sama babu ƙaƙƙautawa a dukkan yankunan Gaza, lamarin da ke ta jawo mace-mace da jikkata Falasɗinawa.
0750 GMT — UNRWA tana makokin ma'aikatanta 63 da aka kashe a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba
Hukumar Ayyuka da Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta yi makokin ma'aikatanta 63 da aka kashe a Gaza sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kai wa tun daga 7 ga watan Oktoba.
"Babu wata kalma da za ta fayyace irin baƙin cikin da muke ciki na kashe ma'aikatanmu na UNRWA 63 a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba," kamar yadda UNRWA ta wallafa a shafinta na X.
"Dole ne a yanzu a kawo ƙarshen wannan kashe-kashe da wahalhalun da ake sha a kullum," hukumar ta ƙara da cewa.
Ta ce duk da dumbin barazanar da ma'aikatanta ke fuskanta, UNRWA za ta ci gaba da yi wa mutanen da ke cikin buƙata hidima a Gaza.
UNRWA ita ce babbar hukumar MDD da ke aiki a Gaza.