Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Pakistan na tuhumar tsohon firaiministan kasar Imran Khan da laifin karbar cin hanci lamarin da ya sanya aka tsare shi.
Jami’an gwamnati na zargin Khan da matarsa da karbar filaye na miliyoyin daloli a matsayin cin hanci ta hannun wata kungiyar bayar da tallafi.
Ana zargin su da karbar cin hancin daga wani babban dan kwangila da ke kasuwancin gidaje a Pakistan.
Khan da dukkan mataimakansa sun musanta aikata laifi.
Mai gina gidajen ya musanta wannan zargi a baya, kuma a ranar Larabar nan ba a iya samun sa ta wayar tarho ba, sannan manajansa na tallata kayayyaki bai amsa gayyatar yin bayani da aka yi masa ba.
Ga wasu bayanai game da kungiyar bayar da tallafin da kuma batun mallakar filayen:
Wace kungiya ce ta ‘Al Qadir Trust’?
'Al Qadir Trust', wata kungiya ce da ba ta gwamnati ba da ke taimaka wa mutane, wadda Bushra Wattoo, matar Khan ta uku ta kafa a lokacin da yake matsayin firaiminista a 2018.
A lokacin da yake firaiminista, Khan ya rika tallata wannan kungiya a tarukan gwamnati.
Ministan Shari’a na Pakistan Azam Nazeer Tarar ya bayyana cewa mata da mijin ne kada shugabannin kungiyar.
Wadanne ayyuka kungiyar ke yi?
Kungiyar na gudanar da wata jami’a a wajen birnin Islamabad wadda ke koyar da Addinin Musulunci tsantsa, wadda matar Khan da aka fi sani da Bushra Bibi ta kafa. An fi saninta a matsayin malamar addini da ke warkar da mutane ta hanyar addu'o’i.
Khan ya bayyana ta a matsayin shugabarsa ta addini, kuma tana taimaka masa wajen bin hanya madaidaiciya a addinance.
Wanne ne batun cin hanci da rashawar?
Ministan harkokin cikin gida na Pakistan Rana Sanaullah ya shaida wa taron manema labarai cewa wannan kungiya na aiki a madadin Khan.
Tana karbar filaye masu daraja a matsayin cin hanci daga mai kasuwancin gini da sayar da gidaje, Malik Riaz Hussain, wanda ke daya daga cikin manya kuma mafiya karfin fada a ji a fannin kasuwancin Pakistan.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta aika sammaci ga Khan da Hussain a shekarar da ta gabata kan su bayar da ba’asi game da bayar da kyautar filayen.
Kungiyar na da wani fili mai girman kusan kadada 60 a kusa da gidan Khan da ke kan dutse wanda ya kai dala miliyan 24.7 da kuma wani karamin filin a Islamabad.
Filin da ke gundumar Jhelum ta jihar Punjab ne filin jami’ar, amma ba a yi wani gini da yawa a cikin sa ba.
Ministar Yada Labarai ta Pakistan Marriyum Aurangzeb ta yi korafi game da gudunmawar da aka bayar don yin gini a jami’ar.
A wata sanarwa da ministar ta fitar ta ce “Kungiyar ta karbi Rupee miliyan 180 (Dalar Amurka 630,460) don gudanar da ayyuka a jami’ar, amma bayanai sun nuna cewa an kashe Rupee miliyan 8.52 (Dalar Amurka 28,020) ne kawai.
Ta yaya aka gano badakalar cin hancin?
Gwamnatin Pakistan ta bayyana cewa al’amarin ya faro ne da dala miliyan 240 da aka dawo da su Pakistan daga Birtaniya a 2019, bayan da Hussain ya yi asarar kadarori da makudan kudade don warware wani bincike da ake yi masa a Birtaniya kan ko kudin na halal ne ko na haram.
An bayyana cewar maimakon a saka kudaden da aka dawo da su a asusun gwamnatin Pakistan, sai gwamnatin Khan ta yi amfani da su don biyan tarar da kotu ta ci Hussain saboda mallakar kadarorin gwamnati a farashin da yake kasa da darajarsu a birnin Karachi.
Ministan harkokin cikin gida ya kuma zargi Hussain da bayar da filaye a Jhelum da Islamabad ga kungiyar ‘Al Qadir Trust’ don biyan wancan abu da aka yi musu.