Mai gabatar da ƙara na kotun ICC Karim Khan na neman sammacin kama Benjamin Netanyahu da Yoav Gallant. /  Hoto: AA

Mai gabatar da ƙara na kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Ƙasa da Ƙasa (ICC) ya ce ya samu wata barazana a lokacin da yake gudanar da bincike kan manyan jami'an Isra'ila, inda wani babban jami'i ya shaida masa cewa an kafa kotun ne domin Afirka da 'yan daba irin su Putin ba wai don ƙasashen Yamma da ƙawayenta ba.

A wata hira da ya yi da kafar CNN, Karim Khan ya ce: "Na samu wasu zaɓaɓɓun shugabanni da suka yi magana da ni kuma sun fito ƙarara sun ce 'wannan kotu an kafa ta ne don Afirka da kuma 'yan daba irin su Putin', abin da wani babban shugaba ya gaya mani kenan," in ji shi.

"Ba haka muke aiki ba," in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa "Kamata ya yi a ce wannan kotu ta zama gatan dokoki, yadda za ta iya hukunta mai ƙarfi da azzalumi."

Sammacin kama Netanyahu

Kotun ta ICC dai na neman sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaron Ƙasar Yoav Gallant tare da shugabannin Hamas Yahya Sinwar da Ismail Haniyeh da kuma Mohamed Deif.

Zarge-zargen da ake wa Netanyahu da Gallant sun haɗa da ''laifin kisan ƙare-dangi da kuma amfani da yunwa a matsayin makamin yaƙi ta hanyar hana kayan agaji da kuma kai hare-hare na ganganci kan fararen hula a rikicin,'' in ji shi.

Laifukan da ake tuhumar Sinwar da Haniyeh da kuma Deif da aikatawa sun haɗa da "kisan kiyashi da kuma yin garkuwa da mutane da fyaɗe da cin zarafi a lokutan zaman gidan yari," kamar yadda Khan ya shaida wa CNN.

"Babu wanda ya fi ƙarfin doka," in ji shi.

Ya ba da shawarar cewa idan Isra'ila ba ta amince da kotun ta ICC ba, "suna da 'yanci su ƙalubalanci hurumin da ke gaban alƙalan kotun, wannan ita ce shawarata a gare su."

Kudurin Majalisar Dinkin Duniya

Isra'ila na ci gaba da kai munanan hare-hare a zirin Gaza duk da ƙudurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya buƙaci a tsagaita wuta cikin gaggawa a yankin.

Sama da Falasdinawa 35,500 ne aka kashe tun daga lokacin, waɗanda akasarinsu mata ne da kananan yara, yayin da wasu sama da mutum 79,600 suka jikkata tun daga watan Oktoban da ya gabata, sakamakon martanin da ya wuce gona da iri kan harin da ƙungiyar Hamas ta kai Isra'ila.

Harin na Hamas ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 1,200 tare da yin garkuwa da wasu ɗaruruwa.

Fiye da watanni bakwai da yaƙin na Isra'ila, lunguna da saƙon Gaza da dama sun lalace a cikin wani yanayi da hana shiga da abinci da ruwan sha mai tsafta da kuma magunguna.

Ana tuhumar Isra'ila da kisan kiyashi a Kotun Duniya ta ICJ, inda aka umarce ta da ta tabbatar da cewa dakarunta ba su aikata kisan kiyashi ba tare da ɗaukar matakan tabbatar da cewa an kai kayan agaji na jinkai ga al'umma fararen hula a Gaza.

AA