Hukumar ba da agajin gaggawa ta Turkiyya (AFAD) ta raba buhunhunan garin fulawa ga iyalai a Gaza yayin da matsalar ƙarancin abinci ke ƙara munana saboda hare-haren da Isra’ila ke kaiwa da kuma takunkumin da ta ƙaƙaba wa yankin da aka yi wa ƙawanya.
Falasɗinawan da ke neman mafaka a sansanin ‘yan gudun hijiran Nusayrat a tsakiyar Gaza sun yi layi a cibiyar raba kayayyaki ga Falasɗinawa ‘yan gudun hijira ta hukumar ba da agaji ta Majasalir Ɗinkin Duniya (UNRWA) domin karɓar fulawar da AFAD ta tura.
Wata uwa da ke kula da iyalinta mai ‘ya’ya goma ta ce wannan shi ne buhun garin fulawan da ta karɓa a karon farko cikin kwanaki 65. Ta bayyana ƙalubalen ciyar da ‘ya’yanta, waɗanda a cikinsu akwai mai buƙata ta musamman bayan ta shafe kwanaki tana ba su fankon kwanukan abinci.
"Mun yi haƙuri da hare-haren bama-baman, mun yi haƙuri da mutuwa, amma ba za mu iya haƙuri da yunwa ba," in ji ta.
Yaƙin da Isra’ila ta shafe kwanaki 425 tana yi a Gaza ya kashe aƙalla Falasɗinawa 44,502 tare da jikkata sama da Falasɗinawa105,454.
Hare-haren bama-baman babu ƙaƙƙautawa sun janyo lalacewar asibitoci da makarantu da muhimman ababen more rayuwa lamarin da ya jefa yankin cikin matsananciyar matsala.