Mutane a yankin nahiyar Arewacin Amurka, tun daga bakin teku a Mexico zuwa gefen Kwazarin Niagra da ke iyakar Amurka da Canada, sun bibiyi kusufin rana suna shewa. A jihar Arkansas ta Amurka mutane sun yi tururuwar suna bikin ɗaurin aure.
A inda sama take wasai, 'yan kallon da ke wuraren da husufin ya wuce sun kalli yadda Wata ya fito tamkar baƙar ƙwallo da ta rufe rana a hankali a hankali, har ya rufe ta ruf, ta yadda sai ƙyallin gefenta ake gani a ranar Litinin.
Wannan ne kusufi na farko da aka gani a nahiyar Arewacin Amurka tun shekarar 2017.
Yayin da duniya ta yi duhu a yankin North Hudson da ke Jihar New York, ɗaruruwan mutane sun yi shewa saboda kaɗuwa.
Wasu suna cewa, "Wayyo Allahna!", yayin da ma'aunin zafi ya ragu kuma fitilu suka kunnu saboda zaton dare ne ya yi.
Garin Mazatlan da ke da wurin shaƙatawa na bakin teku a Mexico, shi ne babban wajen da 'yan kallo suka taru, cikin jerin wuraren da ake iya ganin kusufin.
Dubban mutane sun yi cincirindo a gefen teku suka zauna kan kujeru sanye da tabarau da ake kallon rana da shi. An kunna kiɗan fim ɗin "Star Wars" lokacin da sama ta yi duhu bayan da wata ya yi wa rana labule.
Ga wasu hotunan yadda kusufin ya kasance! 👇