The Al Shifa hospital is the largest health facility in Gaza. Photo: AA

1702 GMT — 'Harin Isra'ila ya shafi dakunan kwanciyar marasa lafiya a asibitin Al Shifa'

Harin wata tankar yaƙi ya shafi dakunan da marsa lafiya ke kwance a asibitin Al Shifa, a cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza.

Sojojin Isra'ila sun kai hari kan sashin kula da masu ciwon zuciya da tankar yaƙi, inda suka kai hari a dakunan marasa lafiya na asibitin Al Shifa," in ji ma'aikatar lafiya a wata gajeriyar sanarwa.

Ta kara da cewa harin tankar ya shafi sashen kula da masu ciwon zuciya na asibitin. Sannna kuma harin ya lalata sashen tiyata da ke asibitin.

1515 GMT — 'Isra'ila ta kai hari majalisar dokokin Gaza'

Sojojin Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a ginin Majalisar Dokokin Falasdinu da ke Gaza, kamar yadda wasu kafafen yada labaran kasar suka ruwaito da kuma bidiyoyin da ke yawo a intanet.

Kafofin yada labarai da suka hada da gidan talabijin na Channel 12 da jaridar Times ta Isra'ila sun ce sojojin sun lalata ginin majalisar, kwanaki bayan daukar hoton kansu a cikinsa.

1324 GMT - Sojojin Isra'ila sun kori yara da marasa lafiya daga Asibitin Al Shifa: Jami'in asibiti

Sojojin Isra'ila sun kori kananan yara da marasa lafiya da abokan aikinsu daga Asibitin Al Shifa "da kafa," kamar yadda Mohammed Zaqout, shugaban asibitocin Gaza, ya fada a wani taron manema labarai da aka yi a gaban asibitin Nasser da ke Khan Yunis a kudancin Gaza.

Ya ce, "har yanzu wasu majinyata 650 a kwance a asibitin, ciki har da 22 da ke sashe na masu na masu fama da tsananin ciwo, baya ga jarirai bakwai 36 da har yanzu suke kwance a asibitin," in ji shi.

Zaqout ya lura cewa akwai "aƙalla ma'aikatan kiwon lafiya 400 da kuma mutane 2,000 da suka rasa matsugunansu a asibitin da suke buƙatar kulawa da kuma kwashe su cikin aminci.

Ya dora alkahin "kare lafiyar ma'aikatan kiwon lafiya da dubban marasa lafiya, da ƴan gudun hijira da yara a kan Isra'ila."

1240 GMT — Sojojin Isra'ila sun kama karin Falasdinawa 78 a Gabar Yamma da Kogin Jordan

Sojojin Isra’ila sun kama karin Falasdinawa 78 a Gabar Yamma da Kogin Jordan a ranar Laraba, kamar yadda wata kungiya mai zaman kanta ta bayyana.

A wata sanarwa da kungiyar Palestinian Prisoner’s Society ta fitar, ta bayyana cewa daga cikin wadanda aka kama har da wasu mata 17 na jami’a daga birnin Hebron.

Zuwa yanzu sama da mutum 2,650 Isra’ilar ta kama a Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

1030 GMT — Isra'ila ta tayar da bam a ginin karkashin kasa na Asibitin Al-Shifa

Marasa lafiya a Gaza

Sojojin Isra’ila sun tayar da bam a ginin karkashin kasa da ke Asibitin Al-Shifa, jim kadan bayan sun kutsa cikin asibitin.

Sojojin sun afka bangaren kula da masu ciwon koda sa’annan “suka tayar da bam a ginin karkashin kasa,” kamar yadda wata majiya ta likitoci ta tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Tun da safiyar Laraba Isra’ila ta tabbatar da shiga harabar asibitin Al-Shifa da ke Gaza, wanda shi ne asibiti mafi girma a Gaza.

0855 GMT — Jiragen yakin Isra'ila sun kashe Falasdinawa hudu a wani gida

Akalla mutum hudu aka kashe a lokacin da jirgin yakin Isra’ila ya kai hari kan wani gida da ke kusa da wata mafaka a arewacin Gaza a ranar Laraba, kamar yadda Ministan Harkokin Cikin Gida ya bayyana.

Jiragen yakin Isra'ila na ci gaba da luguden wuta kan Gaza. Hoto/Reuters. Hoto: Reuters

Kafafen watsa labarai sun ruwaito cewa Isra’ila ta kai hari kan wani gida da ke sansanin ‘yan gudun hijira da ke Jabalia.

Dubban gidaje ne daga ciki har da asibitoci da masallatai da coci-coci Isra’ila ta lalata a hare-haren da take ci gaba da kai wa Gaza.

0820 GMT — Isra’ila ta ce an kara kashe mata soja biyu a Gaza

Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa an kashe karin sojojinsu biyu a Gaza, wanda hakan ya kawo adadin sojojinsu da aka kashe zuwa 49.

A sanarwar da sojojin suka fitar, sun bayyana cewa karin sojoji hudu aka raunata a yayin da ake ci gaba da gudanar da rikici a Falasdinu.

Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare Gaza inda zuwa yanzu ta kashe sama da mutum 11,400 a Gaza.

0615 GMT — Dakarun Isra’ila sun afka cikin asibitin Al Shifa

Dakarun Isra'ila sun afka asibitin Al Shifa na Gaza a ranar Laraba da safe bayan sun shafe lokaci suna harba rokoki da makamai a asibitin

Shugaban asibitin Dakta Ahmad Mikhallalati wanda shi ne shugaban asibitin mafi girma a Gaza a wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa a yanzu haka tankokin yaki Isra’ila da buldoza na cikin harabar asibitin.

Tun da farko a ranar Laraba da safe, sojojin Isra’ila sun tabbatar da cewa sun kaddamar da hari kan Asibitin Al-Shifa.

0550 GMT — Dakarun Houthi sun ce sun kai hari kan Isra'ila a ranar Talata

Kungiyar Houthi a ranar Talata da dare ta bayyana cewa ta kai hari da makamai masu linzami kan Isra’ila.

“Sojojinmu sun harba makamai masu linzami a wurare daban-daban da Isra’ila ta mamaye a yankunan Falasdinu,” in ji mai magana da yawun kungiyar Yahya Saree.

Dakarun Houthi na Yemen da kuma kungiyar Hezbollah ta Lebanon na taya dakarun Hamas yaki da Isra'ila. Hoto/Reuters

Ya bayyana cewa daga cikin wuraren da asuka kai hari akwai wasu “muhimman wurare” da ke kudancin birnin Eilat.

Saree ya ce kungiyar ta Houthi ta lashi takobin kai hari kan duk wani jirgin ruwan Isra’ila a cikin Tekun Bahar Maliya ko duk wani wuri da za su iya kaiwa.

0304 GMT — 'Dole a kare asibitoci da marasa lafiya' : Fadar White House

Dole a kare asibitoci da majinyatan da ke cikinsu "dole ne a kiyaye su," a cewar Fadar White House a lokacin da aka tambaye ta game da harin da ƙawarta Isra'ila ta kai a babban asibitin Gaza na Al Shifa.

"Ba za mu yi magana a kan takamaiman aikin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da yi ba. Kamar yadda muka ce, ba ma goyon bayan harin sama da ake kai wa kan wani asibiti, kuma ba ma son ganin musayar wuta a asibitin da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba suke, wadanda ba su da mataimaka.

"Mutane, marasa lafiya da ke ƙoƙarin samun kulawar jinya da suka cancanta a kula da su, amma suna samun kansu a cikin tashin hankali. Dole ne a kiyaye asibitoci da marasa lafiya, "in ji mai magana da yawun Kwamitin Tsaro na Fadar White House.

0104 GMT — Hamas ta zargi Biden yayin da Isra'ila ta afkawa asibitin Al Shifa na Gaza da tankunan yaki

Jarirai bakwaini na cikin halin mutu kawakwai rai kwakwai. Hoto: Reuters

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce ta ɗora alhakin kai farmakin da sojoji ƴan mamaya na Isra'ila suka kai a Asibitin Al Shifa, a kan Shugaba Biden" yayin da sashen ƴan ƙuna na asibitin ya ce tankunan Isra'ila na cikin ginin a yanzu haka.

Da sanyin safiyar yau Laraba Hamas ta ce sanarwar da hukumar leken asirin Amurka ta fitar, inda Amurka ta goyi bayan matakin da Isra'ila ta dauka na cewa mayakan Hamas na gudanar da ayyukansu a Asibitin Al Shifa, "wani ƙarin haske ne" kan kutsen da aka yi a asibitin.

"Amincewar Fadar White House da Ma'aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon kan labarin karya na Isra'ila, da ke ikirarin cewa Hamas na amfani da Asibitin Al Shifa don tsara kai hare-hare, alama ce da ke nuna cewa ƴan mamayar za su ci gaba da yi wa farare hula kisan kiyashi," in ji Hamas.

TRT Afrika da abokan hulda