Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a Gaza a kullum waɗanda aksarinsu yara ne da mata. / Hoto: Reuters / Photo: AFP

1225 GMT — Akalla karin Falasdinawa 37 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza, wanda ya kai adadin wadanda suka mutu tun bara zuwa 44,466, in ji ma’aikatar lafiya a yankin da aka yi wa kawanya.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu 105,358 sun samu raunuka a harin da ake ci gaba da kaiwa.

Ma'aikatar ta ce: Sojojin Isra'ila sun kashe mutum 37 tare da raunata wasu 108 a kisan gillar da aka yi wa iyalai hudu a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

0716 GMT — Sojojin Isra'ila sun buɗe wuta a kudancin Lebanon duk da yarjejeniyar tsagaita wuta

Sojojin Isra'ila a safiyar Litinin sun buɗe wuta kan garin Naqoura da ke kudancin Lebanon, wanda wannan ce saɓa yarjejeniya ta baya-bayan nan da Isra'ilar ta yi bayan an cim ma yarjejeniyar a makon da ya gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Lebanon ya ruwaito cewa sojojin na Isra'ila sun buɗe wuta ta hanyar amfani da bindiga mai sarrafa kanta.

Kamar yadda ƙirgar Anadolu ta bayyana, sojojin Isra'ila sun saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta sau 11 a ranar Lahadi inda suka rinƙa kai hari cikin garuruwan Lebanon.

2246 GMT — Kungiyar Fatah ta Falasdinawa ta bayyana cewa tana tattaunawa a birnin Alkahira da kungiyar gwagwarmaya ta Hamas kan shawarwarin da Masar ta gabatar dangane da sake bude mashigar Rafah.

Wani jami'in Fatah, Abdullah Abdullah, ya shaida wa Anadolu cewa "Fatah na da sha'awar ganin an kawo karshen yakin da Isra'ila ke yi a zirin Gaza cikin gaggawa, tare da gaggauta kai kayan agaji da kuma fara sake gina kasar."

“Tawagar Fatah tana nan a birnin Alkahira inda take tattaunawa da tawagar Hamas kan shawarwarin Masar da suka shafi sake bude mashigar Rafah (tsakanin Gaza da Masar) da kuma ganin hukumar Palasdinawa ta kula da shi a bangaren Falasdinu.

TRT Afrika da abokan hulda