Majalisar wucin gadin kasar Haiti ta naɗa Garry Conille a matsayin sabon firaministan kasar, a cewar shugabanta Edgard Leblanc Fils.
Conille, wanda mambobi shida cikin bakwai da suke da ikon yin zabe a majalisar mai wakilai tara suka zaɓa, ya taɓa riƙe muƙamin firaminista daga watan Oktoban 2011 zuwa Mayun 2012 a lokacin mulkin Shugaba Michel Martelly, kuma a halin yanzu shi ne daraktan hukumar UNICEF na yankin Latin Amurka da Caribbean.
Wata ɗaya da ya gabata ne aka nada Michel Patrick Boisvert a matsayin firaministan riƙon ƙwarya bayan da Ariel Henry ya yi murabus a watan Afrilu saboda yawan tashe-tashen hankula da suka mamaye kasar.
Tun a ranar 29 ga watan Fabrairu, wasu gungun masu tayar da zaune tsaye suka yi wa filayen jiragen sama da Ofisoshin 'yan sanda da ma'aikatun gwamnati da gidajen yari da sauran cibiyoyin gwamnatin ƙasar ƙawanya.
Ƙungiyoyin 'yan daban ne ke suke riƙe da mafi yawan wurare a babban birnin kasar Port-au-Prince, kuma su ne suke take hakkokin ɗan'adam da suka hada da cin zarafi da kisan kai da garkuwa da mutane da kuma azabtarwa.
Babu firaminista a ƙasar a lokacin da rikicin ya barke
Rikicin ya barke ne a daidai lokacin da firaministan ƙasar Henry ya bar Haiti zuwa Kenya don halartar shirin kammala aikin tura jami'an 'yan sanda 1,000 da za su taimaka wajen sake ƙwato iko da yankin na Caribbean.
Firaministan bai samu damar komawa ƙasar ba sakamakon hare-haren, kuma an rufe filin tashi da sauƙar jiragen sama na babban birnin ƙasar kusan watannin uku da suka wuce.
Ana sa ran tura tawagar da Kenya ke jagoranta, wadda Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bai wa izini zuwa ƙasar a watan Oktoban 2023.
A baya-bayan nan ne shugaban kasar Kenya William Ruto ya gana da shugaban Amurka Joe Biden a birnin Washington, wanda ya yi alkawarin tallafa wa shirin aikin.
Conille ya yi karatu a fannin likitanci da lafiyar jama'a kana ya yi aiki a yankuna masu fama da talauci a Haiti, inda ya taimaka wajen daidaita ayyukan sake gina su bayan mummunar girgizar kasa a shekarar 2010 da ƙasar ta fuskanta.
Ya yi aiki na tsawon wasu shekaru a Majalisar Dinkin Duniya kafin a nada shi Firaminista amma bai cika shekara guda ba ya yi murabus saboda rashin jituwa tsakaninsa da shugaban kasar da majalisar ministocinsa.
Zai jagoranci kasar ta yankin Caribbean har sai an gudanar da babban zabe a karshen shekara mai zuwa.