Wani harin jirgi mara matuki da Isra'ila ta kai kan wani gida ya kashe mutane akalla uku tare da jikkata wasu da dama a Gaza, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka bayyana.
Harin bam din da aka kai wani gida da ke Khan Yunis da sanyin safiyar Alhamis, ya yi sanadin jikkata mutane da dama, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasdinu na WAFA.
Gidan da aka kai harin ya ruguje tare da barnata dukiyoyi da dama da ke kewaye, a cewar WAFA .
Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci a gaggauta kawo karshen kisan fararen hula, yana mai kira ga dukkan bangarorin da su yi taka-tsantsan.
Kazalika a ranar Alhamis din, dakarun sojin Isra'ila sun kai hare-hare kan kungiyar ‘yan ta’adda da ke ikirarin jihadi inda suka kashe wani babban kwamandanta Ali Ghali yayin da aka kai hari gidansa.
A cewar rahoton kafar yada labaran Falasdinu, an yi niyyar kai harin ne a kasan wani ginin gidan bene a kudancin Gaza, inda aka kashe akalla mutane biyu ciki har da kwamandan.
Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce mutane 23 ne suka mutu tun bayan barkewar fadan a ranar Talata, inda wasu manyan mayakan kungiyar ta masu ikirarin jihadi uku da fararen hula akalla 10 wadanda akasarinsu mata da kananan yara ne suka mutu.
Isra'ila ta himmatu wajen kara harba makamin roka a daidai lokacin da rahotanni ke nuna kokarin da Masar ke yi wajen ganin an tsagaita wuta.
Wannan dai shi ne fada mafi muni da ake gwabzawa tsakanin Isra'ila da mayakan Falasdinu a Gaza a baya bayan nan, kuma daga cikin wadanda suka mutu har da mata da kananan yara.
Hare-haren na zuwa ne a lokacin da ake kara samun tashe-tashen hankula da rikice-rikice a shekarar da ta gabata a yankunan Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
An gaza yin sulhu yayin da ake ci gaba da gwabza fada
Bayan kazamin fada da aka gwabza a ranar Laraba, sannan aka yi ta luguden wuta na rokoki kan kudanci da tsakiyar Isra'ila da kuma kai hare-hare ta sama a Zirin Gaza, wani gidan talabijin na Masar ya sanar cewa kasar tana shiga tsakani don bangarorin biyu su tsagaita wuta.
Amma yayin da aka ci gaba da kai hare-haren har zuwa safiyar ranar Alhamis, alamu sun nuna cewa babu wani bangare da ya yi shirin ja da baya.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana kai hare-hare ne kan ‘yan ta’adda ne kawai, amma kuma an kashe kananan yara daga cikinsu har da dan shekara hudu.
Kakakin rundunar sojin kasar Daniel Hagari ya shaida wa gidan rediyon sojin Isra'ila cewa kashi hudu na makaman roka da aka harba a lokacin wannan fadan sun fada ne a Gaza, inda suka kashe akalla mutane hudu ciki har da wata yarinya 'yar shekaru 10.
Isra'ila ta ce hare-haren da aka kai ta sama na ramuwar gayya ne kan harba rokoki da kungiyar masu ikirarin jihadi ta yi a makon jiya bayan mutuwar daya daga cikin 'ya'yanta da suka yi yajin kin cin abinci a lokacin da suke tsare a Isra'ila.
Isra'ila ta ce tana kokarin kauce wa rikici tsakaninta da Hamas tare da takaita fadan da ake gwabzawa.
Laifuka a yakin Isra'ila
Isra'ila ta fuskanci suka daga kasashen duniya dangane da yawan fararen hula da aka kashe a ranar Talata, wadanda suka hada da matan kwamandojin kungiyar masu jihadi su biyu da wasu daga cikin 'ya'yansu da wani likitan hakori da ke zaune a daya daga cikin gine-ginen da aka kai hari tare da matarsa da dansa.
A tashe-tashen hankulan da suka faru a baya, kungiyoyin kare hakkin bil adama sun zargi Isra'ila da aikata laifukan yaki sakamakon yawan mutuwar fararen hula da aka samu.
Isra'ila ta ce tana iya kokarinta don kaucewa asarar rayukan fararen hula tare da dora alhakin hare-haren kan kungiyoyin da ke dauke da makamai saboda suna zaune ne a wuraren da jama'a ke da yawa.
Rasa rayuka a yankunan Kogin Yamma
Tashin hankalin na baya bayan nan ya zo ne a daidai lokacin da aka cika shekaru biyu da kazamin yakin kwanaki 11 da aka kwashe ana gwabza fada tsakanin mayakan Gaza da Isra'ila.
Mai magana da yawun kungiyar Hamas, Abdul Latif al Qanou, ya fada a ranar Laraba cewa "Hare-haren na daga cikin matakan mayar da martani ga kisan kiyashin da Isra'ila ta yi".
A ranar Laraba, sojin Isra'ila suka kai farmaki garin Qabatiya da ke gabar Yammacin Kogin Jordan, inda suka kashe mutane biyu wadanda sojin suka zarga da kai musu hari.
Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta bayyana sunayen mutane biyun da Ahmed Jamal Tawfiq Assaf, mai shekaru 19 da kuma Rani Walid Ahmed Qatanat, mai shekaru 24.
Rikicin na baya-bayan dai ya sanya adadin Falasdinawa da aka kashe ya kai 132 a rikicin Isra'ila da Falasdinu a bana.