Mutum fiye da 80 sun mutu yayin da daruruwa suka jikkata a kasar Yemen da ke fama da yaki yayin daya daga cikin turmutsutsu na karbar sadakar kudi mafi muni da ya faru a kasar, a cewar jami'ai na kabilar Houthi.
Iftila'in ya faru ne ranar Laraba a kasa mafi talauci ta yankin kasashen Larabawa kwanaki kadan kafin Sallar Idi.
Akalla mutum "85 sun mutu sannan fiye da mutum 322 sun jikkata" bayan turmutsutsun a lardin Bab al Yemen da ke birnin na Sanaa, a cewar wani jami'in tsaro na Houthi.
Ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "mata da kananan yara na cikin wadanda suka mutu," ko da yake ba ya so a ambaci sunansa saboda ba a ba shi damar yin magana da 'yan jarida ba. Wani jami'in na daban ya tabbatar da adadin mutanen da suka mutu.
Wani wakilin AFP ya ce lamarin ya faru ne a wata makaranta da ake rabon sadakar kudi a yankin da ke hannun Houthi na birnin nan Sanaa.
Ganau sun ce daruruwan mutane ne suka taru domin karbar sadakar kudin.
'Yan kabilar Houthis masu rike da makamai sun rika harbi a sama a yunkurin shawo kan dandazon mutanen da suka taru, sai dai harbe-harben sun fada kan wasu wayoyin lantarki da suka yi bindiga sannan suka shafi jama'ar da ke wurin, a cewar wasu ganau, Abdel Rahman Ahmed da Yahia Mohsen.
Hakan ne ya sanya mutane suka dimauce suna ta guje-guje abin da ya haifar da turmutsutsi, in ji su.
An kai mutanen da suka mutu da wadanda suka jikkata asibitocin da ke kusa da wurin sannan an kama mutanen da suke rabon kudin, a cewar wata sanarwa da ma'aikatar cikin gida ta fitar, wadda kamfanin dillancin labaran Saba ya rawaito.
Shugaban bangaren siyasa na 'yan tawayen Houthi Mahdi al Mashat ya ce an kafa kwamiti domin yin bincike kan musabbabin turmutsutsun.