Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan (Tsakiya) a lokacin da Firayim ministan Malaysia, Anwar Ibrahim (a dama ) ke tabarsa a lokacin da ya isa birnin Kuala Lumpur / Hoto: AA

Firaministan Malaysia, Anwar Ibrahim, ya tarbi Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wani bikin da aka yi a hukumance.

A birnin Putrajaya, Erdogan da Ibrahim za su tattauna ranar Talata kuma za su halarci wani zama tsakanin tawagoginsu domin tattaunawa kan dangantaka tsakaninsu da kuma batutuwan duniya, ciki har da yaƙin da ake yi a Gaza.

Bayan an yi bikin rattaba hannu kan yajejeniyoyi, za su halarci wani taron manema labarai.

Daga baya, Erdogan zai gabatar da jawabi ga ƙungiyar haɗaka ta ‘yan kasuwar Turkiyya da Malaysia.

A ranar Lahadi ne, Erdogan ya fara wata ziyara ta kwana huɗu zuwa ƙasashen Malaysia da Indonesia da kuma Pakistan.

Ya gabatar da wani jawabi ranar Litinin a Jami’ar Malaya, inda aka ba shi Digirin-Digirgir na girmamamawa.

"Duk da nisan da ke tsakaninsu, Turkiyya da Malaysia, waɗanda suke ɓangarori daban-daban na nahiyar Asia, haƙiƙa suna ƙawance, ‘yan'uwa ne kuma ƙasashe ne da ke tare," in ji shi.

TRT World