An kai Falasɗinawa Asibitin Al-Aqsa Martyrs bayan da suka jikkata sakamakon harin da Isra'ila ta kai sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke Deir al Balah a Gaza ranar 13 ga watan Yunin 2024. / Hoto: AA

1017 GMT —Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe a yaƙin Gaza sun kai 37,232

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,232 a watanni takwas da ta kwashe tana kai hare-hare a yankin, a cewar Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Falasɗinu.

Cikin waɗanda suka mutu har da mutum 30 da dakarun Isra'ila suka kashe a awanni 24 da suka wuce, in ji ma'akatar ta Kiwon Lafiya/

Ta ƙara da cewa Isra'ila ta jikkata mutum 85,037.

0714 GMT —Dakarun Isra'ila sun ƙara kutsawa cikin Rafah

Tankokin yaƙin Isra'ila sun ƙara kutsawa cikin yammacin Rafah, a yayin da suke yin luguden wuta ta sama da ƙasa da ruwa, inda suka tilasta wa dubban iyalai ficewa daga yankin da tsakar dare, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

Sun ce dakarun Isra'ila sun kutsa zuwa yankin Mawasi na Rafah da ke kusa da bakin teku, wanda aka ayyana a matsayin tudun-mun-tsira a dukkan sanarwar da sojojin Isra'ila suka fitar tun da suka ƙaddamar da hare-hare a Rafah a watan Mayu.

Wata sanarwa da rundunar sojojin Isra'ila ta fitar ta musanta ƙaddamar da hare-hare a yankin na Mawasi.

Hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniya a yayin da dakarun Isra'ila suke yin luguden wuta a Rafah. / Hoto: Reuters

2138 GMT — Hamas ba ta ga wata alama daga Isra'ila ta amincewa da shawarar Biden kan tsagaita wuta a Gaza ba

Hamas ta ce ta nuna "cikakken haɗin-kai" a yunƙurin tsagaita wuta a mamayar da Isra'ila take yi wa Gaza amma ta zargi Sakataren Wajen Amurka Antony Blinken da haɗa baki da ƙoƙarin "ɗora mana laifi da kawo tarnaƙi a yarjejeniyar".

A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar mai fafutukar kare hakkin Falasɗinawa ta yi kira ga Amurkwa, wadda ita ce babbar ƙawar Isra'ila, ta matsa lamba kan Isra'ila don amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindina a yankin.

Hamas ta ce yayin da jami'an Amurka suka bayyana cewa Isra'ila ta amince da shirin tsagaita wuta da Shugaba Joe Biden ya gabatar ranar 31 ga watan Mayu, "ba mu ji jawabi daga kowane jami'in Isra'ila da ya tabbatar da ya amince da shirin ba."

Tun da farko, wani jami'in Hamas Taher al-Nunu ya zargi Blinken da nuna son kai, yana mai cewa yana kalamai da ke nuna tamkar shi ne ministan harkokin wajen Isra'ila.

"Ba shi da adalci. Ba shi da dattako. Yana yin baki-biyu. Yana son nuna cewa ƙungiyar Falasɗinawa ce take ƙoƙarin yin ƙafar-ungulu a wannan yarjejeniya," in ji al-Nunu a hira da Al Jazeera.

An kai Falasɗinawa Asibitin Al-Aqsa Martyrs da ke Deir al-Balah sakamakon jikkatar da suka yi a harin da Isra'ila ta kai a sansanin 'yan gudun hijira na Bureij / Hoto: AA

2120 GMT — Houthi ta kai harin bam kan wani jirgin ruwa a yakin Bahar Maliya

Ƙungiyar Houthi ta ƙasar Yemen ta ƙaddamar da harin ban kan wani jirgin ruwan kasuwanci a yankin Bahar Maliya, a cewar hukumomi.

Kakakin rundunar sojojin Yemen, Birgediya Janar Yahya Saree, ya ce su suka kai harin, yana mai cewa jirgin ruwan mai ɗauke da tutar ƙasar Liberia, mallakin kamfanin Tutor na ƙasar Girka ne.

Ya ce sun kai harin ne da "jirgin ruwa maras matuƙi," da jirage marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami.

A wani saƙon gargaɗi da ta aike wa masu safarar jiragen ruwa, Cibiyar da ke sanya ido kan Sojin Ruwa ta Birtaniya, ta bayyana cewa an kai hari kan wani jirgin ruwa a yankin Hodeida da ke ƙarƙashin 'yan Houthi.

TRT Afrika da abokan hulda