1230 GMT — Faɗa ya rincaɓe a birnin Gaza bayan ba da umarnin kwashe jama'a
An gwabza kazamin fada da ruwan bama-bamai a birnin Gaza da wasu yankunan Falasdinawa a yau Juma'a yayin da masu shiga tsakani ke ci gaba da kokarin dakatar da yakin da ya shiga cikin wata na goma.
Shugaban Amurka Joe Biden ya fada a taron Ƙungiyar Tsaro ta NATO a birnin Washington jiya Alhamis cewa jami'an diflomasiyyar Amurka, duk da matsalolin da ake fuskanta, suna samun "ci gaba" tare da masu shiga tsakani na kasa da kasa wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tare da jaddada cewa "lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan yaki".
Kafofin yada labarai masu alaka da mahukuntan yankin Hamas, sun ce sojojin Isra'ila sun kaddamar da sabbin hare-haren sama fiye da 70.
Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta ba da rahoton mutuwar mutum 32, tana mai cewa "an kai waɗanda suka mutun, wadanda akasarinsu yara da mata ne zuwa asibitoci cikin dare, saboda kisan kiyashin da ake ci gaba da yi".
Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana kuma gwabza fada a yankin Rafah da ke kudancin kasar, inda dakarunta suka "kawar da 'yan ta'adda da dama a hare-hare ta sama".
2227 GMT — Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga ƙungiyar ƙawance ta NATO ta ƙara matsa wa Firminisatan Isra'ila Benjamin Netanyahu lamba don tabbatar da cewa an samu tsagaita wuta da kuma shigar da kayan jin ƙai ba ƙwaƙƙautawa zuwa yankin Gaza da aka mamaye.
Erdogan ya zargi Netanyahu da jefa Isra'ila da ma duka ƙasashen yankin cikin haɗari saboda manufofinsa na mamaya da ganganci.
Ya kuma ƙara da cewa Turkiyya ba za ta amince da duk wata haɗaka tsakani NATO da Isra'ila ba har sai an shimfiɗa gamsasshen tsarin zaman lafiya a Falasɗinu.
"Matuƙar ba a shimfiɗa tabbatacce kuma dawwamammen tsarin zaman lafiya a Falasɗinu ba, to duk wani yunƙurin haɗaka da Isra'ila ba zai samu amincewar Turkiyya ba," a cewar Erdogan a wajen taron manema labarai a taron NATO
2300 GMT — Dole ne a kawo ƙarshen yaƙin da Isra'il ke yi a Gaza yanzu - Biden
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce dole ne a kawo ƙarshen yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza yanzu, yana shaida wa 'yan jarida cewa Isra'ila da Hamas duk sun amince da shirinsa na tsagaita wuta, sai dai ya ƙara da cewa har yanzu akwai sauran kafofin da za a toshe su.
"Isra'ila da Hamas duka sun amince kan wannan shirin. Don haka na aika tawagata zuwa yankin don tsara yadda za a yi aiki da shi," kamar yadda Biden ya faɗa a wajen wani taron manema labarai.
"Waɗannan batutuwa ne masu wahala, masu sarƙaƙiya. Har yanzu akwai sauran kafofin da sai an toshe su. Muna samun ci gaba. Sakamakon yana da kyau. Na ƙudiri aniyar ganin an yi aiki da ƙudirin da kawo ƙarshen yaƙin nan, wanda dole ne a kawo ƙarshensa yanzu," kamar yadda Biden ya ce.