Erdogan ya jinjina wa ƙungiyar Hamas bisa cika alƙawuran da ta ɗauka na yin musayar fursunoni da Isra'ila, duk kuwa da cewa ta yi ƙoƙarin keta yarjejeniyar. . / Hoto: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jaddada cewa babu wani mai ƙarfin iko da ya isa ya tilasta wa mutanen Gaza ficewa daga ƙasarsu ta “dindindin”, domin kuwa yankin Gaza da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Ƙudus yankuna ne mallakin Falasɗinawa.

"Babu wani mutum da yake da ikon fitar da mutanen Gaza daga ƙasarsu, wadda aka kafa dubban shekaru. Yankin Falasɗinu, wanda ya haɗa da Gaza, Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Ƙudu, na Falasɗinawa ne," in ji Recep Tayyip Erdogan a hira da manema labarai ranar Lahad a Istanbul kafin ya tashi zuwa ƙasar Malaysia.

Shawarar da shugaban Amurka Donald Trump ya bayar game da da kwashe Falasɗinawa daga yankin Gaza, bayan shan matsin lamba daga Yahudawa masu tsaurin ra'ayi, ba batu ne da ya kamata a tattauna a kansa ba, in ji Shugaba Erdogan.

Kazalika Erdogan ya jinjina wa ƙungiyar Hamas bisa cika alƙawuran da ta ɗauka na yin musayar fursunoni da Isra'ila, duk kuwa da cewa ta yi ƙoƙarin keta yarjejeniyar.

Game da halin da ake ciki a Syria, Shugaba Erdogan ya ce ana ci gaba da tono manyan ƙaburbura a sassa daban-daban na Syria, lamarin da ke ƙara tona asirin gwamnatin Assad.

Shugaban Turkiyya ya bayyana fatansa na ganin an samu zaman lafiya a Syria a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Ahmed Alsharaa, yana mai cewa nan ba da jimawa ba ƙasar za ta samu kwanciyar hankali.

Babu gurbin ƙungiyoyin 'yan ta'adda a Syria, in ji Erdogan, wanda ya jaddada cewa shugaban Syria Ahmad Alsharaa zai yi yaƙi da waɗannan ƙunguyoyi.

TRT World