Wata motar daukar marasa lafiya da sauran motoci na tafiya a wata hanya mara kyau bayan hatsarin da ya faru na jirgin da ke dauke da Shugaban Iran Ebrahim Raisi, a yankin Azerbaijan ta Gabas. / Hoto: Reuters

An gano gawar Shugaban Iran Ebrahim Raisi da ministan harkokin wajen ƙasar da sauran jami’ai a wajen da jirgi mai saukar ungulu ya yi hatsari, bayan an shafe sa’o’i ana nemansu a wani yanki mai tsaunuka da rashin kyawun hanya a arewa maso yammacin ƙasar, a cewar kafar watsa labaran gwamnati.

Gidan talbijin na ƙasar bai bayar da bayanai kan dalilin hatsarin jirgin ba a yankin Azerbaijan ta Gabas a Iran.

Mataimakin Shugaban Iran kan Lamuran Zartarwa Mohse Monsouri shi ma ya tabbatar da mutuwar shugaban na Iran.

Wani jami’in gwamnatin yankin ya yi amfani da Kalmar “faɗuwa” amma sauran sun yi amfani da ko dai kalmar “sauka mai wahala” ko kuma “hatsari” wajen bayyana abin da ya faru.

Wasu hotuna da IRNA ya fitar da safiyar Litinin sun nuna abin da kamfanin dillacin labaran ya bayyana a matsayin inda hatsarin ya faru, a wani waje mai ciyayi sosai.

Sojoji da suke magana da yaren Turkic na yakin sun ce: “Ga shi can, mun gano shi.” Jim kadan bayan nan kuma, gidan talabijin din kasar ya ringa sanya wani rubutu da ke cewa: “Babu alamun akwai wanda yake a raye daga cikin mutanen da ke cikin jirgin.”

Bai yi ƙarin bayani ba, amma wani kamfanin dillacin labarai da ke da alaƙa da gwamnati Tasnim ya nuna masu ceto suna amfani da wani karamin jirgi mara matuƙi a wajen da hatsarin ya faru, suna magana a tsakaninsu su ma suna faɗar irin waɗannan kalaman.

Bidiyon ya nuna jelar jirgin da kuma tarkacensa a kusa da shi. Babban gidan talabijin na ƙasar ya ringa sanya addu’o’i ba ƙaƙƙautawa.

TRT World