Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a Faransa domin nuna bijirewa ga irin gallazawar da 'yan sanda suke yi wa jama'a, inda aka yi arangama tsakanin masu gangamin da jami'an tsaro a gefen birnin Paris.
An gudanar da zanga-zanga a fadin kasar ne wata uku bayan wata mummunar zanga-zanga da aka yi sakamakon kisan da 'yan sanda suka yi wa wani matashi da ya ki tsayawa a wurin bincike ababen hawa a Paris.
A babban birnin kasar, masu gangamin -- manya da kanana -- sun rike kwalayen da aka rubuta "A daina gallaza wa jama'a", "Ba za mu manta da abin da ya faru ba" da kuma "Masu wanzar da doka suna kisa".
Masu zanga-zangar sun nuna adawa da dokar tsaro mai lamba 435-1, wadda aka kafa a 2017, wacce ta bai wa jami'an tsaro damar harbe duk mutumin da bai bi umarninsu ba.
Kungiyoyin da suka gudanar da zanga-zangar sun yi kiyasi cewa fiye da mutum 80, 000 ne suka amsa kiransu a fadin kasar ta Faransa, ciki har da mutum 15,000 a Paris, sai da ma'aikatar cikin gida ta ce mutum 31,000 ne suka shiga zan-zangar a fadin kasar, wadanda suka hada da mutum 9,000 a Paris.
'Tarzomar da ba za a yarda da ita ba'
Gwamnati ta yi Allah wadai da "tarzomar da ba za a yarda da ita ba" da aka yi a gefen birnin Paris, bayan an kai hari kan motar 'yan sanda inda aka makure biyu daga cikinsu, in ji wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP.
Daruruwan mutane daga cikin masu zanga-zangar sun sanya kyallayen da suka rufe fuskokinsu inda suka balle daga wurin zanga-zangar suka warwatsu a Paris.
Sun rika fasa tagogin bankuna suna jifan motar 'yan sanda da ke kusa da shingen bincike ababen hawa, a cewar wakilin AFP.
Rundunar 'yan sanda ta ce an jikkata uku daga cikin jami'anta.
"Muna ganin abin da kyamar 'yan sanda yake nufi," a cewar Ministan Cikin Gida Gerald Darmanin a sakon da ya wallafa a X, wanda a baya ake kira Twitter, yana mai yin tir da "tarzomar nuna kyama" ga 'yan sanda.
Shugaban 'yan sandan Paris Laurent Nunez ya ce an kama mutum uku.
Jimilla, an kama mutum shida a fadin Faransa, a cewar wasu bayanai daga Ma'aikatar Cikin Gida ta kasar.
'Rashin adalci yana wargaza iyali'
Cikin wadanda suka yi zanga-zanga a birnin Lille har da Mohamed Leknoun, mai shekara 27, wanda 'yan sanda suka kashe dan uwansa Amine a watan Agustan 2022 bayan ya ki bin umarninsu.
"Duk irin wannan rashin adalcin yana wargaza iya," in ji shi a hirarsa da AFP.
Ya ce har yanzu hukumomi ba su sanar da shi komai ba game da matakin da ake bi a binciken da ake yi wa dan sandan da ya kashe dan uwansa.