Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka, NASA, za ta kawo samfurin dutsen astiriyod mai yawo a samaniya zuwa duniyar Earth ranar 24 ga watan Satumba, ƙarƙashin Shirin OSIRIS-REx.
Jirgin sama jannati na shirin, wanda ya yi tafiyar kusan kilomita 44,500 a duk sa'a ɗaya a yayin da ya shigo sararin duniya, zai ajiye rokar da ke ɗauke da samfurin dutsen Bennu da ɓurɓushin ƙurarsa a dajin Utah, inda masana kimiyya suka ƙagara da jiran karɓarsu.
Rokar da ta ɗauko samfurin za ta sauka a doron ƙasa ne da misalin ƙarfe 8:55 na safe agogon Amurka. Nauyin samfurin dutsen na Bennu ya kai akalla giram 250, wanda shi ne samfurin dutsen astiriyod mafi girma da aka taɓa kawowa duniya.
Wani babban mai bincike Dante Lauretta ne yake jagorantar shirin OSIRIS-REx na NASA, wanda farfesa ne a kimiyyar al'amuran sauyin yanayi da sama jannati a Jami'ar Arizona da kuma dakin gwaje-gwaje na al'amuran Duniyar Wata.
An yi amannar Dutsen Bennu na dauke da arzikin wasu ma'adanai kuma shi ne astiriyod da ya fi shawaginsa a kusa da Duniyar Earth.
Ana sa ran samfurin dutsen da aka ɗebo zai buɗe damarmakin bincike na gomman shekaru, tare da bai wa masana kimiyya damar gano amsar yadda duniyoyi ke samuwa da kuma yadda rayuwa ke farawa a cikinsu.
Sannan ana tsammanin gano yadda tekunan Duniyar Earth suka samu ruwansu, da kuma zurfafa fahimtar ɗan'adam a kan duwatsun asitiriyod da ka iya cin karo da Earth.
Wani labarin mai alaƙa: Duniyarmu ta Earth na dab da fadawa hatsari tana kaucewa daga muhallinta mai aminci
Girman Bennu da yadda yake zagaye a sararin samaniya ya sa yake da hadari da yiwuwar jawo wani mummunan abu nan gaba.
Duk bayan shekara shida sai dutsen ya wuce ta farfajiyar Earth daga nisan kilomita kusan 300,000 a sararin samaniya, inda yake zuwa kusa da ita sosai fiye da nisanta da wata, kuma akwai yiwuwar zai iya cin karo da duniya sau ɗaya a cikin karo 2,700 na wucewarsa.
CIn karon nasa da Earth ka iya faruwa nan da watan Satumban shekarar 2182, a cewar bayanan tawagar masana kimiyya na OSIRIS-REx.
A shekarar 1999 aka fara gano dutsen, sai aka saka masa suna Bennu, wato sunan wani abun bauta mai tsohon tarihi a Masar, da ake alaƙantawa da rana da halittu da haihuwa.
Dutsen Bennu wanda faɗinsa ya kai kusan mita 492 — inda ya ɗan fi faɗin tagwayen ginin Empire State Building na Malaysia — ya fi shekara biliyan 4.5 a tarihince.
Ana alaƙanta shi da cewa wani tsohon ɓurɓushi ne na fashewar unguwarmu ta rana, wanda shi ne dalilin da ya sa masana kimiyya ke tunanin wasu sinadarai da ke jikinsa sun yi tasiri wajen samuwar rayuwa a Duniyar Earth.
Shirin OSIRIS-REx na NASA ba shi ne na farko da ya kawo samfurin astiriyod Earth ba.
A watan Yunin shekarar 2010, shirin Hayabusa na Hukumar Bincike a Sararin Samaniya ta Japan (JAXA) ya kawo samfurin wani dutsen astiriyod na Itokawa, yayin da shirin Hayabusa2 na JAXA kuma ya kawo kusan giram biyar na samfurin dutsen astiriyod daga Ryugu a watan Nuwamban 2021.
An ƙaddamar da jirgin sama jannatin OSIRIS-REx wanda girmansa bai wuce motar bas mai ɗaukar mutum 15 ba a ranar 8 ga watan Satumban 2016.
Ya fara bulaguronsa na dawowa Duniyar Earth na tsawon shekara biyu da rabi a watan Mayun 2021, bayan da ya yi nasarar ɗauko samfurin dutsen Bennu a watan Oktoban 2020.