China na shirin inganta hadin gwiwarta da kasashen Afirka a ayyukan haro da samar da zaman lafiya da dai sauransu. Hoto: Reuters

China ta bayyana shirin kasar wajen inganta hadin gwiwa tsakanin sojojinta da kasashen Afirka, matakin da zai kara tabbatar da matsayinta na zama daya daga cikin manyan abokan cinikayya da ci gaba a nahiyar.

Ministan tsaron kasar Li Shangfu ne ya bayyana hakan a yayin taron birnin Beijing karo na uku kan zaman lafiya da tsaro, inda ya jadadda cewa hadin gwiwa tsakanin China da kasashen Afirka zai inganta tsaro da zaman lafiyar duniya.

"A nan gaba, China za ta inganta hadin gwiwar sojinta da kasashen Afirka a fannoni daban-daban da suka hada da atisayen hadin gwiwa da kiyaye zaman lafiya da koyar da ayyukan soji da kuma ba da horo don samun kwarewar tunkarar duk wani rashin tabbas na yawan tashe-tashen hankula da duniya ke fuskanta ," a cewar ji Li a zaman taron.

Kusan wakilai 50 daga kasashen Afirka da kungiyoyin shiyya-shiyya ne ke halartar taron tsawon kwanaki shida a wannan mako.

Cude-ni-in-cudeka

"China ita ce kasa mafi girma da ke tasowa kuma Afirka ita ce nahiyar da ta fi kasashe masu tasowa, kasar dai ta kuduri niyyar tsayin daka tare da al'ummar Afirka don aiwatar da shirin samar tsaro ga duniya da kuma gina al'ummar China da Afirka mai makoma daya," in ji Li.

A shekarar 2022, China ta zuba sabon jarin kai tsaye a Afirka na dala biliyan 3.4, a yanzu haka dai kasar ita ce ta hudu mafi girma a zuba jari a Afirka, kuma akwai kamfanoni sama da 3,000 na kasar da ke nahiyar, a cewar ma'aikatar ciniki ta kasar.

A watan Afrilun bara ne Shugaba Xi Jinping na kasar ya gabatar da shirin samar da tsaro a duniya.

Manufar shirin ita ce kawar da tushen duk wani rikicin kasa da kasa da kuma inganta harkokin tsaron duniya da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe don samar da ingantaccen zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a duniya," in ji Li.

TRT Afrika