China ta kira wannan cinikin makaman da gagarumin katsalandan kan harkokin cikin gidanta. Hoto/AP

Ma’aikatar tsaro ta Taiwan ta bayyana cewa China ta tura gomman jiragen yaki da jiragen ruwa kwanaki bayan da Amurka ta amince da wata yarjejeniya ta dala miliyan 500 domin sayar wa Taiwan din makamai.

Sanarwar da ta fitar a ranar Asabar ta nuna cewa jirage 32 daga sojojin na China da kuma jiragen sojin ruwa na shawagi tsakanin shida na safe a ranar Juma’a zuwa Asabar shida na safe.

Daga cikin wadannan, jiragen sama ashirin ko dai sun ratsa ta iyakar da ta raba mashigin ruwan Taiwan ko kuma ratsawa ta iyakar tsaro ta sama ta Taiwan din.

Sai dai Taiwan ta bukaci jiragenta na sama da na ruwa da na’urorin harba makamai masu linzami su mayar da martani kan lamuran, kamar yadda ma’aikatar tsaron Taiwan din ta bayyana.

China ta bayar da himma kan atisaye

China na kallon Taiwan a matsayin wani lardi nata da ya balle wanda ta ce akwai yiwuwar ta kwace shi da karfi idan ta kama.

A shekarar da ta gabata, Beijing ta kara bayar da himma kan atisayen soji a kusa da tsibiri domin mayar da martani kan lamuran siyasa da Taiwan din ke shiga.

A makon da ya gabata, China ta kaddamar da atisaye domin “ya zama gargadi” bayan mataimakin shugaban Taiwan din ya tsaya a Amurka a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Paraguay.

Ma’aikatar wajen Amurka a ranar Laraba ta bayyana cewa ta saka hannu kan siyan wasu na’urori da suka shafi jirgin yaki na F-16 ga Taiwan kan kudaden da suka kai dala miliyan 500.

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron China Zhang Xiaogang a ranar Juma’a ya bayyana cewa China na adawa da siyan wadannan makamai, inda ya kira lamarin da "babban katsalandan" kan harkokin cikin gida na China.

Haka kuma Zhang ya ce China ta kuma bukaci Amurka da ta cika alkwarin da ta dauka na kin goyon bayan samun ‘yancin kan Taiwan.

AP