Gwamnatin Birtaniya ta amince ta ci gaba da sayar wa Isra'ila makamai, a cewar Sakataren Harkokin Wajen ƙasar David Cameron, yana mai yin watsi da masu matsa musu lamba kan su dakatar da sayar mata makaman da take aikata kisan ƙare-dangi a Gaza.
"Game da batun Isra'ila da dokokin jinƙai na duniya, kuma yadda dokokin sayar da makamai na Birtaniya suke, na yi nazari kan shawarwari na baya-bayan nan kan batun Gaza da kuma yaƙin da Isra'ila take yi a can," in ji Cameron yayin wata ziyara da ya kai Washington ranar Talata.
"Nazarin da muka yi na baya-bayan nan ya nuna cewa matsayinmu kan sayar da makamai bai sauya ba," kamar yadda ya shaida wa wani taron manema labarai na haɗin-gwiwa da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken.
"Amma ina so na bayyana ƙarara cewa, muna ci gaba da nuna matuƙar damuwa game da rashin jinƙai a Gaza."
Ita ma Amurka, wadda ita ce ƙasar da ta fi sayar wa Isra'ila makamai, ta yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi mata na dakatar da sayar wa Isra'ila makamai duk kuwa da ƙorafin da ta daɗe tana yi kan yadda Firaminista Benjamin Netanyahu yake tafiyar da yaƙin Gaza.