Birtaniya ta tura kashin farko na masu neman mafaka zuwa Rwanda, a cewar jaridar The Sun, tana mai cewa an fitar da mutanen daga ƙasar ne ranar Litinin.
Mutanen da aka tura Rwanda sun bar Birtaniya ne don raɗin kansu — ba sa cikin waɗanda gwamnatin ƙasar za ta tursasa wa fita daga ƙasar nan da watanni kaɗan masu zuwa, a yunƙurinta na hana neman mafaka a Birtaniya.
Gwamnatin Birtaniya ta ce za ta biya kimanin fam 3,000 ga duk mai neman mafaka da ya amince ya fita daga ƙasar zuwa Rwanda don raɗin kansa a ƙarƙashin wannan tsarin da zummar rage baƙin-hauren da suka cika ƙasar.
Hukumomi a Birtaniya sun kwashe shekaru biyu suna ƙoƙarin warware matsalolin da suka taso - waɗanda suka haɗa da gurfanar da su a kotu da shan suka daga 'yan hamayya - a yunƙurinsu na tura masu neman mafaka ƙasar Rwanda, mai nisan kilomita 6,400 daga Birtaniya, matakin da suke gani zai hana wasu ci gaba da hanƙoron zuwa ƙasarsu.
A makon jiya ne majalisar dokokin Birtaniya ta amince da ƙudurin dokar fitar da masu neman mafaka a ƙasar bayan an yi zazzafar muhawawa kuma Firaiminista Rishi Sunak ya ce yana sa rai za a soma fitar da su zuwa Rwanda nan da makonni 10 zuwa 12.
Mutane da dama sun soki gwamnatin Birtaniya kan aiwatar da wannan shiri wanda ake kallo a matsayin na "nuna wariyar launin fata" wanda ke barazana ga baƙaƙen-fatar ƙasar.
Wata ƙungiya da ke kare hakkin masu neman mafaka ta wallafa saƙo a shafin X da ke cewa mambobinta za su yi gangami a wajen ofishin hukumar shige-da-fice da ke kudancin London domin hana tursasa wa mutane fita daga ƙasar.
Rahotanni daga kafofin watsa labarai sun ce hukumomin Birtaniya za su soma tattara kashin farko na mutanen da za su fitar zuwa Rwanda nan ba da jimawa ba.