Sanarwar ta MDD ta kuma zargi sojojin Isra'ila da kisan gilla da azabtar da jami'an kiwon lafiya da gangan. Hoto: AFP / Photo: AP Archive

Alhamis, 10 ga watan Oktoba, 2024

Wani bincike na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya gano cewa, Isra'ila ta aiwatar da wani tsarin hadaka na lalata tsarin kiwon lafiya na Gaza a yaƙin da take yi a can, matakin da ya hada da laifukan yaki da kuma cin zarafin bil'adama.

Wata sanarwa da tsohuwar shugabar hukumar kare hakkin bil'adama ta MDD Navi Pillay ta fitar gabanin wani cikakken rahoton ta zargi Isra'ila da "kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa a kan jami'an kiwon lafiya da wuraren aiki" a yakin da aka fara bayan da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kai hari a kudancin kasar Isra'ila a ranar 7 ga Oktoban 2023.

"Yara, musamman sun fi shan wahalar wadannan hare-hare, inda rushewar tsarin lafiyar ya fi shafarsu kai tsaye," in ji Pillay, wadda za a gabatar da rahotonta ga babban taron MDD ranar 30 ga watan Oktoba.

Isra'ila ta ce mayakan na Gaza suna gudanar da ayyukansu ne daga wuraren da aka gina gine-gine da suka hada da gidaje masu zaman kansu da makarantu da asibitoci kuma za ta kai musu hari a duk inda suke fakewa.

Hamas ta musanta boye 'yan kungiyar da makamai da ofisoshin kwamandoji a tsakanin fararen hula.

Sanarwar ta MDD ta kuma zargi sojojin Isra'ila da kisan gilla da azabtar da jami'an kiwon lafiya da gangan, da kai hare-hare kan motocin kiwon lafiya da kuma hana marasa lafiya izinin barin Gaza da aka yi wa ƙawanya.

Ta ba da misali da mutuwar wata yarinya Bafalasdiniya Hind Rajab a watan Fabrairu tare da 'yan'uwanta da ma'aikatan jinya biyu da suka zo domin ceto ta daga hare-haren Isra'ila.

Isra'ila ta yi luguden wuta kan UNIFIL a Lebanon, rundunar Qassam ta yi wa sojin Isra'ila kwanton ɓauna a Gaza

1315 GMT — Sojojin Isra'ila sun bude wuta a wurare uku da ke hannun dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kudancin kasar Lebanon, kamar yadda wata majiyar MDD ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, amma ba ta bayyana irin barnar da hakan ta jawo ba.

Majiyar ta ce daya daga cikin wuraren da aka harba shi ne babban sansanin UNIFIL da ke Naqoura.

Wata mai magana da yawun UNIFIL ta bayyana cewa, gobara ta tashi a wurare uku, yayin da wasu dakarun wanzar da zaman lafiya biyu suka samu raunuka.

A kudancin Gaza, reshen sojojin Hamas, Qassam Brigades, sun kai hari kan wani sintiri na leken asiri na Isra'ila da ke kunshe da motoci biyu da sojoji hudu da ke amfani da wani jirgin yaki mara matuki a Khan Younis, a cewar wata sanarwa da aka fitar a tashar Telegram ta kungiyar 'yan adawa.

0730 GMT –– Mazauna sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza sun shiga kwana na biyar a jere na kazamin harin bama-bamai da Isra'ila ke kai musu, da suka hada da shingen da suka saka musu, da lalata gidaje, da kuma tilasta musu gudun hijira.

Tsarin kiwon lafiya na Jabalia na fuskantar karin matsala, inda sojojin Isra'ila suka ba da umarnin kwashe mutane daga wasu manyan asibitoci da suka hada da Kamal Adwan, na Indonesiya, da kuma Asibitocin Al-Awda, inda suka ba su sa'o'i 24 don yin biyayya.

A yau wannan wa'adin ya ƙarewa.

Wannan shi ne karo na uku da aka kai hari a Jabalia tun farkon yakin Isra'ila a Gaza wanda ya fara a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

A ranar Lahadin da ta gabata ne sojojin Isra'ila suka sanar da fara kai hare-hare ta kasa a Jabalia, biyo bayan hare-haren wuce gona da iri kan gabashi da yammacin arewacin Gaza, wanda aka bayyana a matsayin mafi muni tun cikin watan Mayu.

Akalla Falasdinawa 130 ne aka kashe a hare-haren Isra’ila a cikin wannan mako, kamar yadda ofishin yada labaran gwamnati ya bayyana.

A ranar Litinin din da ta gabata ce sojojin Isra'ila suka gargadi mazauna Jabalia, Beit Hanoun, da Beit Lahia da su ƙaura zuwa kudancin Gaza.

A halin da ake ciki, yankunan Beit Lahia, Al-Tawam, da Al-Atatra an ci gaba da kai hare-haren bama-bamai ta sama da ta ruwa da ta ƙasa.

A cewar rahotanni a hukumance na Falasdinu, kusan 700,000 daga cikin mutane miliyan 1.2 mazauna yankunan arewacin Gaza sun zabi zama duk da umarnin ficewa da aka ba su.

Shaidu sun bayyana cewa sojojin Isra'ila sun kewaye yankin sansanin Jabalia, inda aka kai farmakin kasa a safiyar Alhamis.

2129 GMT — Harin da Isra'ila ta kai kan tantuna a arewacin Gaza ya kashe Falasdinawa 16

Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 16 tare da raunata wasu a harin da ta kai ta sama a kusa da Asibitin Al-Saeed Yaman da ke arewacin Gaza da aka yi wa ƙawanya.

Hossam Abu Safiya daraktan asibitin Kamala Adwan da ke Gaza ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu cewa an kashe mutanen ne a lokacin da wani jirgin yakin Isra'ila ya kai hari kan tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu a wajen asibitin.

Jami’an agajin sun ce wadanda suka mutu sun hada da mata da kananan yara, inda suka ƙara da cewa harin bam din ya dagargaza “gawarwakin Falasdinawan da suka mutu."

Bayan haka, an kashe Falasdinawa da dama tare da jikkata wasu a wani hari na biyu ta sama da aka kai kan mutanen da suka rasa matsugunansu a wajen kofar asibitin, kamar yadda hukumar kare fararen hula ta Gaza ta sanar.

Ƙarin labarai 👇

2104 GMT — Isra'ila ta kashe mutum 10, ciki har da likitoci 5, a kudancin Lebanon

Isra'ila ta kashe akalla mutane goma da suka hada da likitoci biyar tare da raunata wasu da dama a kudancin kasar Lebanon.

Hukumar tsaron farar-hula ta kasar Lebanon ta fitar da sanarwa cewa, an kashe ma'aikatanta biyar a harin da Isra'ila ta kai kan cibiyar tsaron fararen hula da ke Derdghaya, garin gundumar Tire da ke lardin kudancin kasar.

Ta ce wadanda abin ya shafa suna bakin aiki a cibiyar kuma a shirye suke su amsa kiran gaggawa.

A halin da ake ciki kuma, Ma'aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan garin Wardaniyeh da ke wannan gunduma ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu 12 na daban, sai dai ba ta fayyace munin raunukan da suka samu ba.

Ma'aikatar ta kara da cewa "ana gano ragowar sauran wadanda abin ya shafa ta hanyar gwajin DNA."

2016 GMT — Shugaban UNRWA ya ce Gaza ta yi sauyawar da ba za a iya gane ta ba

Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ya ce Gaza da aka yi wa kawanya ta kasance “ba za a iya gane ta ba”, kuma babu alamar kawo ƙarshen tashe-tashen hankulan Isra’ila da suka mamaye yankin Gabas ta Tsakiya.

Philippe Lazzarini ya bayyana haka a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan halin da Falasdinawa ke ciki, inda ya ce, shekara daya bayan kazamin yakin Gaza, babu ranar kawo ƙarshen tashe-tashen hankulan da suka dabaibaye yankin.

"Shekara ce ta babbar asara da wahala," in ji shi. "Ba za mu iya ikirarin jahilci kan abin da ke faruwa ba - kuma ba za mu iya yin watsi da abin da ke faruwa ba. Shi ya sa muke sake yin kira ga kwamitin sulhu, da kasashe mambobin kungiyar, su dauki mataki."

TRT World