Biden ya sha alwashin cewa ba zai "miƙa wuya" ga Shugaban Rasha Vladmir Putin ba. / Hoto: Reuters / Photo: AFP

Shugaba Biden ya yi amfani da jawabi ga Ƴan Ƙasa inda ya yi suka kan yadda abokin hamayyarsa Donald Trump yake son ya "mayar da martani da mummunar ramuwar gayya" yayin da yake magana kan "gagarumin farfaɗowar tattalin arziki" a lokacin mulkinsa.

Jawabin na Biden a ranar Alhamis da yamma — da aka yi lokacin da ake tsaka da zanga-zanga don neman tsagaita wuta a Gaza — daga Ginin Majalisar Amurka ya yi gargadi kan "mayar da martani da mummunar ramuwar gayya" a kaikaice yana magana kan Trump.

Biden ya sha alwashin cewa ba zai "miƙa wuya" ga Shugaban Rasha Vladmir Putin ba, sannan ya roƙi majalisar dokokin Amurka ta amince da tallafin soja da ya gabatar mata.

"Putin na Rasha a tafiye yake, yana mamaye Ukraine kuma yana tayar da yamutsi a nahiyar Turai da gaba da nan," a cewar Biden. "Idan wani a ɗakin nan yana zaton cewa Putin zai tsaya a Ukraine, ina tabbatar muku ba zai tsaya ba."

Wanda ya gabace ni, tsohon shugaban ƙasa ɗan Republican, ya fada wa Putin cewa, 'Ka yi duk abin da ka ga dama...ba zan miƙa wuya ba... Ina faɗin haka ne a fayyace, duniya tana kallonmu.

"Rayuwata ta koya min cewa na rungumi ƴanci da dimukuraɗiyya," a cewar Biden lokacin da yake jawabinsa da misalin karfe takwas agogon GMT.

"A yanzu wasu mutane da suke da shekaru irin nawa, wani labarin daban suke ji," yana magana a zahiri kan Trump, duk da cewa bai ambaci sunansa ba. "Wani labarin Amurka na ramuwar gayya, da ƙiyayya da ƙeta. Wannan ba ni ba ne."

An sanar da wata hanyar tallafawa Gaza

A wata alama ta ƙalubale da dama da Biden ke fuskanta, masu zanga-zangar adawa da yadda yake goyon bayan mummunan yaƙin da ake yi a Gaza sun tare jerin motocinsa a hanyarsa ta zuwa ginin Capitol Hill kafin ya fara jawabi.

Masu zanga-zanga da dama sun riƙa kiraye-kiraye a tsagaita wuta inda suka toshe titin Pennsylvania Avenue, hanyar da ake bi daga fadar White House zuwa ginin majalisar dokoki, a cewar wani wakilin AFP.

A ɓangare ɗaya kuma Biden ya bayyana cewa sojojin Amurka za su kafa wata cibiyar ruwa ta wucin-gadi a gaɓar ruwan Gaza yayin da Isra'ila ke ƙara rufe duk wasu hanyoyin zuwa Gaza, har ma ga babbar ƙawarta Amurka wacce ta riƙa jefa kayan agaji ta sama a Gaza, amma dai rahotanni na cewa ta amince da sayar wa Isra'ila kayayyakin soja sau 100 tun daga ranar 7 ga Oktoba.

Biden ya "illar da yaƙin da ake yi a Gaza ya yi wa fararen-hula ya fi gaba ɗaya illar da ya yi musu a duka yaƙe-yaƙen da aka yi a baya idan aka haɗa su waje guda," yana tabbatar da cewa an kashe fiye da mutum 30,000 da suka haɗa da dubban mata da yara.

Ya ce tashar ruwan da za a buɗe ta wucin-gadi a Gaza za ta "ba da damar ƙara yawan kayan agajin" da ake kai wa Gaza, yana mai ƙarawa cewa ba zai yiwu Isra'ila ta yi amfani da agaji a matsayin wani abu da za ta tilasta a yi "yarjejeniya kafin a kai ba."