Shugaban Amurka Joe Biden ya aike da wasika ga manyan 'yan Majalisar Dattawa da Wakilai na kasar, yana nema "Majalisun su amince a sayar wa Turkiyya jirgin yaki samfurin F-16 ba tare da bata lokaci ba," kamar yadda wani jami'in gwamnatin Amurka ya gaya wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Wasikar Biden ta yi maraba da "matakin da majalisar dokokin Turkiyya ta dauka na amincewa Sweden ta zama mamba ta kungiyar tsaro ta NATO" sannan ta shaida wa shugabannin Kwamitin Harkokin Waje na Majalisun Dokokin bukatar gwamnatin Biden "ta neman a sayar wa Turkiyya jirgin yaki samfurin F-16 da zarar an kammala cika tsare-tsare," a cewar jami'in a ranar Laraba.
"Shugaban kasa ya bukaci Majalisun Dokoki su sayar da jirgin yaki samfurin F-16 ba tare da bata lokaci ba," in ji jami'in wanda ba ya so a ambaci sunansa.
Ranar Talata majalisar dokokin Turkiyya ta amince da gagarumin rinjaye Sweden ta zama mamba a kungiyar tsaro ta NATO inda 'yan majalisa 287 suka goyi bayan matakin yayin da 55 suka yi watsi da shi. Yanzu Hungary ce kadai kasar da ke cikin NATO wadda ba ta amince Sweden ta shiga kungiyar ba.
Finland da Sweden — wadanda ke da makwabtaka da Rasha — duka sun nemi shiga kungiyar NATO bayan Rasha ta kaddamar da yaki a Ukraine a watan Fabrairun 2022.