Shugaban Amurka Joe Biden a asirce ya amince a kashe biliyoyin dala domin saya wa Isra'ila sabbin bama-bamai da jiragen yaƙi duk da cewa jami'an gwamnati sun fito fili sun bayyana damuwarsu game da kashe-kashen da dakarun Isra'ila suke yi wa Falasɗinawan Gaza.
Makaman da shugaban Amurka ya amince a saya wa Isra'ila a wannan makon sun haɗa da bama-bamai masu hatsarin gaske samfurin 1,800 MK84 2,000 da samfurin 500 MK82 500, a cewar wasu jami'ai na Ma'aikatar Tsaron ƙasar, a tattaunawarsu da jaridar Washington Post.
A makon jiya, Ma'aikatar Tsaron Amurka ta amince a tura jirgen yaƙi guda 25 samfurin F-35A da injinansu, in ji wani jami'in gwamnatin ƙasar.
An ƙiyasta cewa jiragen yaƙin da injinansu sun laƙume kusan $2.5bn.
Ba a fito fili an bayyana batun sayan makaman ba, haka kuma babu wata sanarwa a shafin intanet na Ma'aikatar Tsaron Amurka dangane da wannan batu.
A ranar Juma'a, Sanata Bernie Sanders ya caccaki gwamnatin Biden kan tura ƙarin makamai zuwa Amurka.
"Amurka ba za ta iya roƙon Netanyahu ya daina jefa bama-bamai kan farar hula ba sai daga baya kuma ta aika masa sama da bama-bamai 2,000 ba da za su iya shafe ginin birni baki ɗaya. Wannan abu ne mara kyau," in ji Sanders a shafinsa na X, kamar yadda Washington Post ta ruwaito.
Wannan na zuwa ne duk da cewa Biden da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a bainar jama'a sun yi ta ce-ce-ku-ce a 'yan makonnin da suka gabata, wanda a baya-bayan nan suka yi arangama bayan da Amurka ba ta sa baki ba a kudirin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya bukaci a tsagaita bude wuta a Gaza.
Netanyahu ya mayar da martani ta hanyar katse ziyarar da ya yi niyyar kaiwa Washington inda aka yi niyyar tattaunawa kan batun Isra'ila ta shiga Rafah. A halin yanzu an daga zaman tattaunawar, sai dai hakan bai sa Biden ya kawar da aniyarsa ta bai wa Isra'ila makamai ba.
Saɓa dokokin Amurka
Makonni biyu da suka gabata, da dama daga cikin ‘yan majalisar dattawan jam’iyyar Democrat sun aika wa Biden wasika suna kira gare shi da ya dakatar da sayar da makamai ga Tel Aviv, saboda a halin yanzu hakan ya saba wa dokar 1961 da ta haramta sayar da makamai ga kasashen da ke hana kai Amurka kai kayan agaji.
Bai kamata Amurka ta ba da taimakon soja ga duk wata kasa da ke kawo cikas ga kai taimakon jin kai na Amurka ba,” in ji Sanata senators Sanders, Chris Van Hollen, Jeff Merkley, Mazie Hirono, Peter Welch, Tina Smith, Elizabeth Warren da Ben Ray Lujan a rubutun da suka yi.
Isra’ila na ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza inda take kashe mutane da raba jama’a da muhallansu.
Netanyahu ya lashi takobin kai hari birnin Rafah wanda ke ɗauke da kusan mutum miliyan 1.5 da suka nemi mafaka a can, duk da cewa an gargaɗe shi kan tsananin buƙatar jin kai da hakan zai haifar.