Fararen hula na kallon yadda Jami'an Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ke binne gawarwakin Falasdinawa da ba a gane su waye ba da suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila.  / Hoto: AFP

Masu ruwa a tsaki na tattaunawa kan tsarin da ya bayar da damar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila, wadda ke kai munanan hare-hare a Gaza tun 7 ga Oktoban 2023.

A karshen makon nan shugabannin hukumomin leken asiri daga Isra'ila da Masar sun gana da Firaministan Qatar, Shaikh Mohammed bin Abdurrahman bin Jassim al Thani, a Paris don tattaunawa kan daftarin mai matakai uku.

Hamas, kungiyar gwagwarmaya da ke rike da iko da Zirin Gaza na Falasdinu a ranar Talata ta tabbatar da karbar kwafin daftarin neman tsagaita wutar.

Wannan wani babban mataki ne mai muhimmanci wajen kawo karshen hare-haren kasa da sama da Isra'ila ke kaiwa Gaza inda ta kashe mutane fiye da 26,000, mafi yawansu mata da yara kanana.

Ga abubuwan da daftarin neman tsagaita wutar ya kunsa.

Matakai uku na warware rikicin

A wata sanarwa da Rueters suka fitar, Hamas ta bayar da kudiri mai matakai uku.

Matakin farko ya kunshi dakatar da rikici da sakin tsofaffi, fararen-hula mata da yara da ake tsare da su, sannan a bayar da damar kai kayan agajin jinƙai, tare da magance matsalolin abinci da lafiya a Gaza.

Mataki na biyu kuma ya hada da sakin sojojin Isra'ila mata, a kara yawan kayan taimako tare da dawo da ayyukan bayar da wutar lantarki da ruwa.

Mataki na uku shi ne na a bayar da gawarwakin sojojin Isra'ila da aka kashe inda su kuma za su mika Falasdinawa fursunonin yaki.

Sanarwar ta fayyace cewa dole ne a dakatar da ayyukan soji daga dukkan bangarorin a dukkan wadannan matakai. Yarjejeniya ce za ta tabbatar da adadin Falasdinawan da ke tsare da za a saki a kowanne mataki, inda za a mayar da hankali kan wadanda suke daure tsawon lokaci.

Idan komai ya tafi yadda ake bukata, yakin zai kawo karshe kuma Hamas za ta sako sojojin isra'ila maza da ta kama, a madadin Falasdinawa da ke daure a gidajen kurkukun Isra'ila.

An aike da wannan shiri zuwa Gaza kuma shugabannin Hamas sun shirya tattaunawa don fitar da matakinsu na karshe.

Me Hamas ta ce game da daftarin?

Kamar yadda shugaban bangaren siyasa na Hamas Haniyeh ya bayyana, "a shirye Hamas take don tattaunawa kan duk wani batu na gaske da wasu shawarwari ko tunani, matukar dai za su kawo karshen hare-haren da ake kai wa."

Da take bayyana babban abin da ta fi bukata, Hamas ta nanata cewa dole ne yarjejeniyar ta kunshi "Cikakken janyewar Isra'ila daga mamayar da ta yi wa Zirin gaza."

Bayanan shugabannin Hamas sun ce shugabancin kungiyar ya samy gayyata zuwa Alkahira don cimma "manufar bai daya" game da yarjejeniyar, kuma a karon farko Haniyeh ya sanar da tafiya Alkahira don tattaunawa kan daftarin.

Amincewar Isra'ila

Labarai da rahotannin da aka fitar sun bayyana cewa wani jami'in Isra'ila da aka boye sunansa ya tabbatar da amincewar gwamnati kan wannan tsari da aka gabatar wa Hamas.

Da yake bayani a unguwar Eli da ke Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye, Netanyahu ya ce: "Ba za mu janye dakarun tsaronmu daga Zirin Gaza ba, kuma ba za mu saki dubunnan 'yan ta'adda ba. Wannan ba zai afku ba."

Netanyahu na fuskantar babbar matsin lamba daga iyalan 'yan Isra'ila da ke tsare a hannun Hamas, suna neman ya cim ma yarjejeniyar ganin an sake su.

Duk da nuna adawa daga netanyahu da gwamnatinsa mai tsaurin ra'ayi, shugaban 'yan adawar Isra'ila kuma tsohon firaminista, Yair Lapid ya bayyana aniyarsa na goyon bayan yunkurin samar da zaman lafiya idan har hakan zai kai ga dawowar wadanda aka kama din.

Ko da dukkan bangarori sun yarda da wannan daftari, tabbatar da musayar fursunonin da cika ka'idojin zai dauki kwanaki.

TRT World