Bai kamata a ƙyale buƙatar shigar Turkiyya cikin Tarayyar Turai a hannun "wasu tsirarun ƙasashe masu manufa ta siyasa ba," in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan.
"Ina so na jaddada cewa bai dace a bar buƙatar Turkiyya ta shiga cikin Tarayyar Turai a hannu wasu tsirarun ƙasashe masu manufa ta siyasa ba," kamar yadda Fidan ya bayyana ranar Laraba a wani taron manema labarai na haɗin-gwiwa da takwaransa na Sifaniya Jose Manuel Albares da suka gudanar a Ankara.
His remarks came after a meeting held by the two ministers in Ankara.
Fidan ya ce tun da farko Sifaniya na cikin ƙasashen da suka yi tsayin-daka wurin goyon bayan Turkiyya domin ta shiga Tarayyar Turai, yana mai jaddada cewa shigar ƙasarsu cikin Tarayyar Turai wani abu ne mai muhmmanci ga gwamnatin Ankara.
Haɗin-kai don samar da tsaro a Bahar Rum
Kazalika ministan harkokin wajen Turkiyya ya ce ƙasarsa da Sifaniya su ne ƙasashe biyu mafi muhimmanci a yankin Bahar Rum, wanda ke fuskantar ƙalubale da suka haɗa da ta'addanci da sauyin yanayi da ƙaura da sauransu.
”Turkiyya da Sifaniya, waɗanda suke gabashi da yammacin Bahar Rum, suna ganin tasirin waɗannan ƙalubale ƙarara. A matsayinmu na ƙasashe biyu da suka kwashe shekaru suna yaƙi da ta'addanci, muna ɗaukar batun haɗin-kai domin bunƙasa tsaro da matuƙar muhimmanci,” in ji shi.
Haka kuma Fidan ya ce za a yi taro na takwas game da dangantakar Gwamnatin Turkiyya da ta sifaniya a watan Yuni.
Dangata da Tarayyar Turai
Turkiyya tana fatan samun kyakkyawar dangantaka tsakanin Ankara da hukumomin Tarayyar Turai inda za a samu ci-gaba mai ɗorewa tare da “kyawawan manufofi ba tare da fatan ganin an yi zaɓen Majalisar Tarayyar Turai mai tsafta,” in ji Fidan.
"Tarayyar Turai a matsayinta na babbar ƙungiya, tana da matsayi babba. A yayin da muke yauƙaƙa dangantaka da Kasashen Turai, muna da mabambantan dangataka da Tarayyar Turai,” kamar yadda ya ƙara da cewa.
Fidan ya ce manufar Ankara kan Tarayyar Turai ba ta sauya ba, musamman bayan da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sake yin nasara a zaɓe a 2023, inda ya jaddada cewa alƙiblar ƙasar ba ta canza ba.
Sifaniya na goyon bayan Turkiyya don shiga Tarayyar Turai
A nasa ɓangaren, Albares ya yaba kan dangantakar da ke tsakanin Sifaniya da Turkiyya a fannin siyasa da tattalin arziki da al'adu.
Ya yi tsokaci kan matsayin Turkiyya a ƙungiyar tsaro ta NATO da buƙatarta ta shiga Tarayyar Turai, yana mai bayyana goyon bayan Sifaniya ga Turkiyya.
“A koyaushe muna goyon bayan tattaunawa tsakanin Turkiyya da Tarayyar Turai kuma muna so a ba ta damar shiga ƙungiyar,” in ji ministan, inda ya jaddada muhimmancin Turkiyya a matsayin babbar ƙawa.
Albares ya shaida wa manema labarai cewa ya yi amanna dukkan ƙasashen Tarayyar Turai za su amince Turkiyya ta zama mamba a cikinsu.