Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta tabbatar da cewa babu wata ɓarna da aka samu a tasoshin nukiliyar Iran bayan zargin Isra'ila da kai hare-hare cikin daren Juma'a.
"IAEA na iya tabbatar da cewa babu wata ɓarna da aka samu a wuraren nukiliyar Iran," in ji hukumar ta shafinta na X a ranar Juma'a.
Darakta-Janar Rafael Grossi na ci gaba da kira ga dukkan ɓangarorin kan su sassauta, kana ya nanata cewa kada makaman nukiliya su kasance abin kai hari a rikicin soji, in ji shi.
Hukumar ta ce suna sa ido sosai kan lamarin.
Isra'ila ta kai wani hari cikin Iran, kamar yadda kafafen yaɗa labaran Amurka da na Iran suka bayyana, amma babu daya daga cikin rahotannin da ya bayyana inda aka kai harin.
Harin dai ya zo ne a matsayin martani ga harin ba-zata da Iran ta kai wa Isra'ila a ƙarshen mako.
Jami’an Amurka da ba a bayyana sunansu ba sun shaida wa kafar yada labarai ta CBS da ABC cewa Isra’ila ta yi amfani da makami mai linzami wajen kai wa Iran hari.
Tashar talabijin din gwamnatin Iran ta tabbatar da cewa an samu tashin bama-bamai a tsakiyar lardin Isfahan, sai dai babu wata tashar nukiliya da harin ya shafa.
Kamfanin dillancin labarai na Mehr ya rawaito cewa an lalata wasu jirage marasa matuƙa uku a sararin samaniyar lardin Isfahan.
"Ya zuwa wannan lokaci dai rundunar sojin Isra'ila ba ta ce uffan ba kan harin, amma ta ce ana gudanar da taron tsaro a Ma'aikatar Tsaron Isra'ila da ke Tel Aviv.
A ranar Asabar ne Iran ta kai hari ta sama kan Isra'ila a matsayin ramuwar gayya kan harin da jiragen saman Isra'ila suka kai kan ofishin diflomasiyyarta da ke babban birnin Siriya a ranar 1 ga watan Afrilu.
Kasar ta harba jiragen sama marasa matuƙa 300 da makamai masu linzami, inda kusan dukkanin tsarin tsaron sama na Isra'ila da ƙawayenta - ''Amurka, Faransa, da Birtaniya'' suka kawar da su.
Isra'ila ba ta dauki alhakin kai harin ba a hukumance, amma ta kai hare-hare kan wuraren da Iran take a fadin Siriya a ƴan watannin nan.
Amurka dai ta musanta cewa tana da hannu cikin hare-haren.
A nata ɓangaren, Isra'ila ta sha alwashin mayar da martani ga ramuwar gayyar Iran.