An kai wasu Falasɗinawa marasa lafiya Asibitin al-Ahli Arab bayan an kwashe su daga Asibitin Kamal Adwan da ke Birnin Gaza, Gaza, ranar 28 ga watan Disamba, 2024. / Hoto: AA

Talata, 31 ga watan Disamba, 2024

1015 GMT — Asibitocin Gaza sun zama 'tarkon mutuwa', in ji shugaban hukumar kare hakkin bil'adama ta MDD Volker Turk, yana mai cewa dole ne a kare su daga yaƙi da rikice-rikice.

"A yayin da ake ci gaba da fuskantar hare-haren bama-bamai babu ƙaƙautawa da kasancewa a cikin yanayi na rashin jinƙai a Gaza, wuraren da suka kamata Falasɗinawa su je domin samun aminci sun zama tarkon mutuwa," a cewar babban jami'in na MDD.

"Kare asibitoci a lokutan yaƙi wajibi ne kuma dole ne duka ɓangarorin su girmama wannan mataki, a kowane lokaci."

0725 GMT — Mayaƙan Houthi sun kai hari da makamai masu linzami a filin jirgin saman Ben Gurion da ke Tel Aviv

Ƙungiyar Houthi ta ƙasar Yemen ta ce mayaƙanta sun kai hari da makamai masu linzami biyu a filin jirgin saman Isra'ila, awanni bayan rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kakkaɓo wani makami da suka harba mata.

"Makami na farko (da aka harba) ya nufi Filin Jirgin Saman Ben Gurion Airport" aTel Aviv, yayin da makami na biyu ya nufi wata tashar samar da hasken lantarki da ke kudancin Birnin Ƙudus, a cewar wata sanarwa da ƙungiyar Houthi ta fitar.

Kazalika ƙungiyar ta ce ta kai hari kan babban jirgin ruwan Amurka mai suna USS Harry S. Truman wanda ke ɗaukar jiragen sama.

Kawo yanzu rundunar sojin Amurka ba ta ce uffan kan wannan ikirari ba.

Ƙungiyar Houthi ta fitar da wani hoto da ke nuna yadda ta kai harin makamai masu linzami a Isra'ila. / Hoto: Reuters

2119 GMT — Matakin da Isra'ila ta ɗauka na rusa asibitoci a Gaza 'kisan kiyashi ne' — rahoto

Matakin da Isra'ila ta ɗauka na rusa asibitocin da ke arewacin Gaza wani ɓangare ne na "kisan kiyashin" da take yi wa Falasɗinawa, kamar yadda jaridar Haaretz da ake wallafawa a Isra'ila ta bayyana a wani sharhi da ta buga.

Jaridar ta soki sojojin Isra'ila kan irin zaluncin da suke aikatawa a arewacin Gaza, tana mai cewa suna yin hakan ne domin hana Falasɗinawa komawa gidajensu.

Jaridar ta ce ruseh-rushen da Isra'ila take yi, musamman na asibitoci, suna tilasta wa mutane tserewa zuwa kudanci domin neman magunguna.

Ta jaddada cewa bai kamata a bar yanki mai girma irin wannan ba tare da asibitoci ba, musamman a lokutan yaƙi, inda ta jawo hankali kan Yarjejeniya ta Huɗu ta Geneva wadda ta buƙaci a kare asibitoci a lokacin yaƙi.

Wasu Falasɗinawa suna duba ɓaraguzan gine-gine bayan Isra'ila ta kai hari a Asibitin Kamal Adwan da ke Beit Lahia / Hoto: AA

Ƙarin labarai👇

0134 GMT — Isra'ila ta ce ta kakkaɓo wani makami mai linzami da aka harba mata daga Yemen

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kakkaɓo wani makami mai linzami da mayaƙa Houthi suka harba mata daga Yemen, lamarin da ya sa aka riƙa kaɗa jiniya a yankunan tsakiyar ƙasar, ciki har da birnin Tel Aviv.

2023 GMT — An yi kutse a shafin X na kamfanin Ford, an wallafa saƙonnin goyon bayan Falasɗinawa

Rahotanni sun bayyana cewa an yi kutse a shafin X na kamfanin ƙera motoci na Ford, sannan aka riƙa wallafa saƙonnin da ke goyon bayan Falasɗinawa.

Saƙonnin da aka wallafa sun haɗa da "A Sakar wa Falasɗinawa Mara", "Isra'ila 'yar ta'adda ce," da kuma "HANKALIN KOWA YANA KAN GAZA."

TRT World