Kafin ya yi rawarsa ta moonwalk, Michael Jackson ya jefa hularsa sama kusa da inda jama'a suka taru. Shekaru 40 bayan haka, za a yi gwanjonta a Paris.
A ranar 26 ga Satumba ne za a yi gwanjon hular a otel din Drouot da ke Paris. Ana sa ran hular za ta tara kudi tsakanin dala 64,000 zuwa dala 107,000.
Duk da cewa tana daga kan gaba a tsakanin kayayyaki 200 da za a baje a wajen gwanjon, mai shirya gwanjon Arthur Perault ta yi ikirarin cewa darajar kayan Jackson sun ragu saboda 'sayar da kayan jabu da na nuna zargi gare shi'.
Tuntuni aka zargi Jackson da ɓata yara kanana, zargin da ya ci gaba har rasuwarsa a 2009, yana da shekaru 50 yana musantawa.
Tafiyar malafar Moonwalk
Sarkin na waka ya yi jifa da hular tasa a yayin da yake shirin bude wakar 'Billie Jean' a 1983. An nuna casun na Motown kai tsaye a wata tashar talabijin.
Daga baya, Jackson ya bayyana 'moonwalk' abun da ya zamo masa babbar lambar sanayya.
Wani mutum da ake kira Adam Kelly ya dauki malafar Jackson, "yana tunanin ma'aikatan mawakin za su zo su karbe ta, amma ba su yi hakan ba," in ji Perault.
Ya ajiye hular a wajensa tsawon shekaru, amma daga baya ta koma hannayen wasu mutanen inda ta kama hanya zuwa Paris.
Sannan akwai wani agogon hannu da mawakin ya fara sakawa a yayin rawar 'moonwalk' a 1983, wanda aka sayar a watan Nuwamban 2009 kan kudi dala 350,000 a yayin gwanjon da aka yi a New York.
Shuhurar da ba a mantawa da ita
Gwanjon da za a yi a ranar 26 ga Satumba a Paris zai gabatar da garayar makadi T-Bone Walker wadda za ta iya samun Yuro 150,000; sannan ga wasu kaya da Martin Gore ya saka su; sannan da wani zinaren Madonna.
Akwai kuma bangorin katangar Bus Palladium, wani waje da aka rufe a Paris a shekarar da ta gabata, wanda shahararrun mawaka suka sanya hannu a kai, wadanda suka hada da The Libertines, Air da The Dandy Warhols, wanda shi ma bangorin darajarsa ta kai daga Yuro 5,000 zuwa 8,000.
Shuhurar waka da mawaka ta zama babban kasuwanci yau a duniya.
Daya daga cikin wadanda suka shirya gwanjon, Lemon a shekarar da ta gabata sun sayar da garayar Noel Gallagher a daren Oasis a Paris, bayan rikici da dan uwansa Liam. An sayar da garayar kan kudi Yuro 385,500.
A wannan watan, kayan da aka yi gwanjonsu na mawaki Freddie Mercury, da suka hada da piano din da ya yi amfani da su wajen hada wakar "Bohemian Rhapsody," sun tara kudi har Yuro miliyan 46.5 a Sotheby bayan da masu saya suka bayyana bukatarsu daga kasashen duniya 76.