Ana sa rai zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump zai yi wasu muhimman naɗe-naɗe a sabon wa’adin mulkinsa na biyu, bayan wasu taruka da wasu da suka tsaya takara, kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka bayyana.
Shugaba Trump yana shirin yin wasu dokokin shugaban ƙasa da sabbin tsare-tsare da dawo da wasu tsare-tsare da zarar ya shiga ofis wanda hakan yake nuni da yadda zai fara aiki gadan-gadan, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CNN ta bayyana.
Sannan ana sa rai galibin mutanen za su samu manyan muƙamai za su halarci taron murnar nasarar da ya samu a garin Palm Beach da ke jihar Florida a ranar Talata kuma sun kammala shirye-shiryensu don kasancewa a wurin.
Trump ya samu nasarar komawa Fadar White House a ranar Laraba, inda ya samu fiye da ƙuri’u 270 na wakilan masu zaɓe kuma yanzu yana da ƙuri’u 295 yayin da ’yar takarar Democrat Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Kamala Harris ta samu ƙuri’u 226, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya bayyana.
Harris ta amsa shan kaye a wani jawabi da ta yi a Jami’ar Howard, wato jami’ar da ta yi karatu.
Mataimakiyar Shugaban Ƙasar ta ce za ta ci gaba da gwagwarmaya don kawo ”’yanci da damarmaki da adalci da kuma mutunta kowa da kowa.
Shugaban Ƙasar Amurka mai barin gado Joe Biden ya yaba mata kan “gaskiyarta” da kuma “jajircewarta” a ranar Laraba bayan ’yar takarar Democrat wato Mataimakiyar Shugaban Ƙasar ta sha kaye a hannun ɗan takarar jam’iyyar Republican Donald Trump.
“Abin da na gani a yau shi ne Kamala Harris ɗin da na sani kuma nake matuƙar ƙauna. Ta kasance abokiyar tafiya ta ƙwarai kuma ta yi wa al’umma hidima da riƙon gaskiya da jajircewa da kuma nuna ɗabi’u masu kyau,” in ji Shugaba Biden kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa bayan Harris ta amsa shan kaye.
Bayan bayyanar sakamakon zaɓen, Shugaba Biden ya kira Trump ta waya a ranar Laraba, inda ya gayyace shi Fadar White House saboda a fara shirye-shiryen miƙa mulki.
Trump ya amsa gayyatar kuma hakan yana nuni da cewa za a miƙa mulki cikin lumana.
“Shugaba Trump ya shirya zuwa ganawar, wadda za a yi nan kusa kuma ya yi godiya kan kiran shi da aka yi,” in ji daraktan yaɗa labarai na kamfe ɗin Trump Steven Cheung.
Shugaban ma’aikatan Biden ya bukaci ɓangaren su Trump da su sanya hannu kan wasu muhimman takardu kafin a fara shirye-shiryen miƙa mulkin, kamar yadda Fadar White House ta bayyana.