Jami'ai da ke sa ido a rufunar zabe sun rufe akwatunan zabe kafin a fara kada kuri'a yayin babban zabe a Karachi na kasar Pakistan a ranar 8 ga Fabrairu, 2024. / Photo: Reuters  

Miliyoyin ƴan ƙasar Pakistan sun soma kaɗa ƙuri'u a babban zaɓen ƙasar da ke cike tashin hankali da ce-ce-ku-ce.

Hukumomin ƙasar sun katse layukan wayar sadarwa a ranar Alhamis a yayin da ake shirin kaɗa ƙuri'u a duk faɗin ƙasar “domin tabbatar da doka da oda” bayan zubar da da jini da aka yi yayin gangamin yaƙin neman zaɓen - ciki har da wasu bama-bamai biyu da suka tashi a ranar Laraba da suka yi sanadin mutuwar mutane aƙalla 29.

Masu sa ido kan zaɓe sun yi hasashen samun ƙarancin fitowar mutane kusan miliyan 128 da suka cancanci kaɗa ƙuri'a a ƙasar, sakamakon kare jini- biri-jini da aka yi a lokacin yaƙin neman zaɓe wanda ya sa aka tsare tsohon firaiministan ƙasar Imran Khan da kuma hana jam'iyyarsa ta Pakistan Tehreek-i-Insaf (PTI) taka rawar gani.

Ana sa ran jam'iyyar Pakistan Muslim League-Nawaz (PML-N) za ta lashe kujeru mafi yawa a zaɓen na ranar Alhamis, masu sharhi sun bayyana cewa Nawaz Sharif mai shekaru 74 wanda ya kafa ƙungiyar, ya shirya tsaf don sake tsayawa takara karo na huɗu.

"Abin da nake tsoro shi ne ko za a ƙirga ƙuri'ar jam'iyyar da na zaɓa," in ji Syed Tassawar, wani mai aikin gine-gine mai shekaru 39, wanda ya kaɗa ƙuri'a a unguwar Noorpur Shahan da ke Islamabad.

"Mu talakawa, ba ruwanmu da wanda zai samu mulki - muna buƙatar gwamnatin da za ta iya shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyaki," in ji shi.

Har ilau a rumfar zaɓen, Haleema Shafiq, ɗaliba a fannin Ilimin Halayyar ɗan'adam mai shekara 22 wadda ta kaɗa kuri'arta a karon farko, ta ce: "Na yarda da dimokuradiyya, ina son gwamnatin da za ta samar wa ƴan mata tsaro a Pakistan."

An buɗe rumfunan zaɓe da misalin karfe 8:00 na safe (0300 GMT) kuma za a rufe da ƙarfe 5:00 na yamma (1200 GMT).

Jami’ai sun tura sama da sojoji 650,000 da ƴan sanda domin samar da tsaro a wuraren zaɓen da tuni tashe- tashen hankula da ruɗani suka mamaye shi.

TRT World