Wani mazaunin New York da yake jin haushin yadda birnin ke karbar 'yan gudun hijira, ya yi amfani da lasifika wajen aike wa da sako mara dadin ji ga makota, inda yake cewa "'Yan gudun hijira ba su tsira a nan ba."
Sakon, wanda aka nade shi a yaruka shida, ya dinga fita tsawon rana daga lasifikar jikin wani gini a babban layin Scott Herkert na yankin Staten, inda ake kira ga 'yan gudun hijirar da su bar wannan yankin, saboda jama'a ba sa son ganin su.
Sakon ya kuma yi kira ga mazaunan wucin gadi da ke cikin wata makarantar Katolika da ta dade babu kowa a ciki da su fice daga wajen. Sakon ya kuma ce akwai beraye da kyankyasai a cikin ginin.
Wannan daya daga cikin hanyoyin nuna wa 'yan gudun hijirar ne cewa ba a maraba da su. Daruruwan masu zanga-zanga sun gudanar da gangami a wajen tsohuwar makarantar, inda suke kira ga gwamnatin garin da ta dauke 'yan gudun hijirar zuwa wani wajen na daban.
Mata da sauran iyalan da aka ajiye a wannan makaranta ta Saint John Villa Academy sun ji wannan sako sosai.
"Dole mu toshe idanuwanmu da rufe idanuwanmu," in ji Aminetou El Alewai, 'yar shekara 39 da ta fito daga Muritaniya kuma ta shiga wannan waje a makon da ya gabata.
"Mu mutanen kirki ne. Ba bata-gari ba ne mu. Mun zo nan saboda matsalolin da ake fama da su a kasashenmu."
A yayin da dubban 'yan gudun hijira ke ci gaba da zuwa New York, mahukunta sun ki samar da sabbin wuraren tsugunar da su, inda suke amfani da makarantu da filayen shakatawa, don aiki da dokar da ta ce lallai a bai wa marasa gidaje wajen da za su tsuguna.
Duk da Tsibirin Staten waje ne da ke dauke da 'yan tsirarun wuraren tsugunar da 'yan gudun hijira, amma dai sun janyo kurari da adawa daga mazauna yankin.
Nuna kyamar ya zo a lokacin da magajin gari Eric Adams ke yin nasa kalaman na nuna adawa ga 'yan gudun hijira, inda ya yi gargadi da cewar za su 'lalata birnin'.
'Yan Jam'iyyar Democratc sun nace kan dole a karbi bakuncin 'yan gudun hijira sama da 100,000 da suka zo birnin, amma shi kuma ya ce kudaden sama musu matsugunai na wucin gadi zai iya kaiwa dala biliyan 12 a shekaru uku masu zuwa.
Adams ya yi watsi da zargin yana amfani da 'yan gudun hijirar a matsayin 'makami' don samun kudade daga tarayya.
An san Tsibirin Staten da tattara masu ra'ayin rikau 'yan Republican a birnin na 'yan Democrat.
Herkert, ma'aikacin Kotun New York na yin amfani da wannan dama inda yake cewa 'Babu dama'.
Da yake zagaya wa a titin unguwarsu da babu kowa, Herkert ya ce sabon matsugunin 'yan gudun hijirar ya lalata shirun da unguwar ke da shi, sannan ya kawo datti da bandakuna zuwa wajen.
A yayin da sakon lasifika a yarukan Sifaniyanci da Rasha da Larabci da Urdu da China da Ingilishi - ke gargadin cewa tsohuwar makarantar na dauke da kwari da dauda, Alewai ta ce ta samu wajen da tsafta, ko da dai ba shi da dadin zama.
A lokacin da Alewai ta tattauna da kamfanin dillancin labarai na 'Assocated Press', makota da ke dauko yaransu daga wata makaranta mai zaman kanta, sun dinga yi musu kallon wulakanci, wasun su ma na yin munanan kalamai ga sabbin zuwa.
"Na ji takaicin abun da wannan matar ke cewa," in ji Alewai. "Na zo New York a matsayin mai neman mafaka, sai suka kawo ni nan. Tabbas ba na jin dadin zama."
Ma'aikata da mazaunan wuraren da aka tsugunar da 'yan gudun hijira sun bayyana cewa masu zanga-zanga sun yi musu barazana, suna saka kida da karfi ko yaushe da dare, in ji wata ma'aikaciya Gabriella Dasilva, wadda kwanakin baya aka fada mata da ta koma kasarta.
Kakakin ofishin Magajin Garin New York, Kayla Mamelak na cewa gwamnatin ta damu matuka da samun labarin yada sakon mara kyau a wajen Makarantar St. John. kuma 'yan sanda na aikin tabbatar da doka da oda a yankin.
Ta ce "Kamar yadda ake fada a ko yaushe, birnin New York na ci gaba da kula da masu neman mafaka."
Dan majalisar jiha David Carr kuma dan Jam'iyyar Republican da ya halarci Makarantar Saint John ya kare sakon murnar, inda ya ce jama'ar mazabarsa na da manyan dalilan da ya sanya su damuwa game da tsadar samar da matsugunai ga 'yan gudun hijirar.
Carr ya ce "Wannan babbar dama ce ga wadanda ba su ji dadi ba da makota da ransu ya baci su bayyana damuwarsu cikin tsari. Suna kokarin tabbatar da an ji amonsu."
John Tobacco, wani dan jarida kuma dan takarar jami'in birni, ya ce yana bayar da hadin kai ga kokarin Herkert, kuma sakon lasifikar ya bayar da ma'ana tare da aika wa da damuwar jama'a.
Ya ce "Akwai damuwa sosai game da mutanen can, suna yin abubuwan da ba su dace ba da suka saba wa hankali da doka."
John Gurriera dan shekara 72 da ke zaune a tsibirin Staten, ya ce bai ji dadin martanin da wasu makotansa suka nuna ba kan wannan abu.
Ya kara da cewa "Nan Birnin New York ne," "Duk mun zo ne daga wasu wuraren."