Faransa na fuskantar rikicewar majalisar dokoki kuma a ranar Litinin din nan za a fara tattaunawar ƙulla yarjejeniyar kafa gwamnati, bayan da jam'iyyar masu sauƙin ra'ayi ta bayar da mamakin yin nasara tare da hana jam'iyyar Marine Le Pen mai tsaurin ra'ayi kafa gwamnati.
Jam'iyyar NFP ta masu sauƙin ra'ayi ta zama wadda ta fi kowacce yawan kujeru a majalisar dokokin Faransa bayan zaɓen na ranar Lahadi, amma babu wata jam'iyya da ta samu adadin kujerun da zai ba ta ikon kafa gwamnati ita kaɗai, sai dai ko a yi ƙawance a kafa gwamnati ko a kafa gwamnati mara rinjaye.
Sakamakon zaɓen ya yi babbar illa ga Shugaba Emmanuel Macron, tare da jefa ƙasa ta biyu mafi ƙarfin tattalin arziki a yankin Turai cikin rashin tabbas na siyasa, a lokacin da ya rage makonni Paris ya karɓi baƙuncin gasar Wasannin Olympics.
Sakamakon zaɓen majalisar dokokin na iya yin illa ga rawar da Faransa ke takawa a Tarayyar Turai, kuma hakan zai sanya da wahala wata jam'iyyar ta iya fitar da wata manufa a cikin gida.
Firaminista ya yi murabus
Babu tabbas kan yadda manufofin Faransa za su kasance a Afirka, inda take fuskantar suka da koma-baya a 'yan shekarun nan saboda abin da da yawan mutane ke wa kallon na zuwa ne saboda yadda take ci gaba da tsoma baki a al'amuran cikin gida na ƙasashen nahiyar tare da kwashe albarkatun ƙasa da arzikinsu.
Jam'iyyar masu sauƙin ra'ayi ta lashe kujeru 182, jam'iyyar Macron ta lashe 168 sannan NR ta Marine Le pen ta lashe kujeru 143, kamar yadda jaridar Le Monde ta bayyana alƙaluman ma'aikatar harkokin cikin gida.
Firaminista Gabriel Attal ya ce zai miƙa takardar yin murabus, amma ba a tabbatar ko shugaban ƙasa zai amince da murabus ɗin nan-take ba, saboda nauyin da ake da shi na kafa sabuwar gwamnati. Attai ya ce zai iya zama a matsayin na riƙo.
"Tabbas zan sauke nauyin da ke kaina matuƙar an buƙaci hakan - ba za a ga saɓanin hakan ba a wannan lokaci da ake dab da karɓar baƙuncin Gasar Olympics da ke da muhimmanci ga ƙasarmu," in ji Attal, a lokacin da ƙawance ƙarƙashin Macron ya tashi a tutar babu.
'Giɓin Ayyukan Majalisar Dokoki'
Jama'ar ɓangaren NFP - sun fito ne daga jam'iyyar Kwaminisanci ta Faransa, jam'iyyar masu sassauƙan ra'ayi, Jam'iyyun Green da Socialist - sun kuma gana kan yadda za su ci gaba da tafiya tare.
Jean-Luc Melenchon madugun 'yan adawa a Faransa ya ce lallai Firaministan zai fito ne daga ƙawancen NFP. Sai dai kuma, ƙawance ba shi da shugaba, kuma kawunan jam'yyun a rarrabe yake kan waye za su zama a matsayin Firaminista.
Wasu sanannun masu matsakaicin ra'ayi da suka haɗa da Edouard Philippe, tsohon firaminista a ƙarƙashin gwamnatin Macron, na cewa a shirye suke su yi aiki don tabbatar da samar da gwamnati tsayayyiya.
Euro ya faɗi haka ne a ranar Lahadi bayan an sanar da sakamakon zaɓen.
"Tabbas za a samu giɓi babba idan aka zo maganar ayyukan majalisar dokokin Faransa," in ji Simon Harvey, shugaban sashen nazari na FX da Monex Europe a Landan.
'Ƙawance mai ban kunya'
Ga jam'iyyar RN ta Le Pe, sakamakon zaɓen ya nesanta da abin da suka gani makonni kaɗan kafin zaɓen a yayin jin ra'ayin jama'a, wanda ya nuna cewa su ne za su lashe zaɓe ba tare da wata matsala ba.
Masu sauki da matsakaicin ra'ayi sun hada kai waje guda bayan zagayen farko na zaben makon da ya gabata inda suka samu adadin da ya kalubalanci RN a zabaye na biyu.
A mayar da martani na karon farko, shugabar RN Jordan Bardella kuma yarinyar Le Pen ta kira ƙawancen masu ƙalubalantar RN da "ƙawance mai ban kunya" inda ta ce hakan zai yi wa Faransa illa.
Akwai yiwuwar Le Pen ce za ta tsaya wa jam'iyyar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, inda take cewar ganin yadda a wannan karon jam'iyyar ta samu ƙuri'u sama da zaɓukan shekarun baya, alamu ne da ke haskaka samun makoma mai kyau a nan gaba.
Ta ce "An jinkirta samun nasararmu ne kawai."
Toshe damar masu ra'ayin riƙau
A yayin da aka faɗa duhu a ranar Lahadi, masu goyon bayan jam'iyyar mai sauƙin ra'ayi sun haskaka mutum-mutumin 'Marianne' a 'Place de la Republique' yayin murnar lashe zaɓe. Marianne wata alama ce ta ƙasa ta Faransa da ke nufin dalili, 'yanci da manufofin jamhuriya.
Baptiste Fourastie, mai zane ɗan shekara 23 da ke Place de la Republique ya bayyana cewa "Ba mu tsammaci haka ba, haka ma sakamakon zaɓen. Muna murnar yadda jama'ar Faransa suka yi nasara ƙaro na biyu ta hanyar toshe damar masu ra'ayin riƙau."
Sai dai kuma, ya bayyana damuwar cewa akwai yiwuwar masu ra'ayin riƙau su ƙara samun karɓuwa tare da lashe zaɓe a nan gaba matuƙar gwamnati mai zuwa ba ta yi abin da ya kamata ba.
Ya ce "Zai yi wahala da majalisar dokoki da ta warwartsu tsakanin jam'iyyu, amma hakan ya fi da a ce tana ƙarƙashin masu ra'ayin riƙau."