Ana yi wa Imran Khan zarge-zarge da dama ciki har da na sayar da kadarorin ƙasa ba bisa ƙa'ida ba. / Hoto: Reuters

An yanke wa tsohon Firaiministan Pakistan Imran Khan da matarsa hukuncin zaman gidan yari na shekara 14 kan samun su da laifin sayar kadarorin ƙasar ba bisa ƙa’ida ba, kamar yadda jaridar Dawn ta ruwaito.

Hukuncin da kotun ta yanke a Islamabad na zuwa ne kwana ɗaya bayan an yanke wa Khan hukuncin zaman gidan yari na shekara 10, mako guda kafin babban zaɓen ƙasar.

Haka kuma wata kotu ta yanke wa Khan hukuncin zaman gidan yari na shekara uku kan sayar da kayayyakin ƙasar waɗanda suka kai sama da rupee miliyan 140 a lokacin da yake minista tsakanin 2018 zuwa 2022.

Duk da cewa daga baya an dakatar da hukuncin, amma Khan na tsare sakamakon zarginsa da hannu a wasu laifukan.

Sai dai Khan ya kafe kan cewa ya sayi kadarorin ne bisa ƙa’ida.

Jami’an gwamnati suna zargin mataimakan Khan sun sayar da kyaututtukan ne a Dubai.

Reuters