An hambarar da Khan ne a zaben raba gardama da aka gudanar a watan Afrilun bara. / Hoto: AA

Jami'an Jam'iyyar Khan ta Pakistan Tehreek-e-Insaf PTI sun bukaci magoya bayan Imran Khan da su fito kan tituna bayan kama shi, amma 'yan sanda sun yi gargadin cewa taron da ya zarce na mutum hudu ya take doka.

‘Yan jam'iyyar PTI ta tsohon Firaiministan Pakistan Imran Khan sun ce an kama shi ne a lokacin da ya gurfana a gaban wata kotu a Islamabad, babban birnin kasar, domin fuskantar tuhume-tuhume kan laifuka da dama.

Fawad Chaudhry, wani babban jami'i cikin jam'iyyar Pakistan Tehreek-e-Insaf ya ce an kama Khan mai shekara 72 a ranar Talata a harabar kotun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar NAB.

An hambarar da Khan ne a zaben raba gardama da aka gudanar a watan Afrilun bara.

Tsarin da ya yi ikirarin ba a yi shi bisa ka'ida ba kuma ya samu makarkashiyar kasashen yamma da suka nuna goyon bayansu ga gwamnatin da ta gaje shi ta Firaminista Shahbaz Sharif.

Chaudhry ya ce an fitar da Khan daga kotu zuwa cikin motar ‘yan sanda. Ya ce a yanzu haka tsohon shugaban yana hannun jami’an tsaro, yana mai yin Allah wadai da kamun da aka yi masa a matsayin "garkuwa."

Gidan Talabijin na GEO mai zaman kansa a Pakistan ya watsa hotunan yadda jami'an tsaro suka tasa keyar Khan zuwa cikin wata motar sulke da ta tafi da shi.

Nan take jam’iyyar Khan ta kai kara gaban babbar kotun Islamabad inda ta bukaci jami’an ‘yan sanda da suka kama shi, su ba da rahoton da ya ba su damar aiwatar da wannan hukunci.

Jami'ai daga hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa sun ce Hukumar NAB ta bayar da sammacin kama Khan a makon da ya gabata kan wata shari'ar ta daban da bai samu beli ba, yanayin da zai iya kare shi daga tsarewar hukuma karkashin dokokin kasar.

‘Zarge-zargen da ba yarda da su ba’

Tsare Khan da aka yi na zuwa ne kwana guda bayan da dakarun soji a kasar suka gargade shi da yin "zarge- zargen da ba su da tushe" bayan da ya sake zargin wani babban jami'i da yunkurin kashe shi.

Amai da ya yi ya lashe a yammacin ranar Litinin ya nuna yadda dangantakar Khan ta tabarbare da dakarun sojin kasar masu karfin fada a ji, wadanda suka goyi bayan hawansa mulki a shekarar 2018, amma kuma suka janye goyon bayansu gabanin zaben da ‘yan majalisa suka yi na raba gardama da ya yi sanadin hambarar da shi.

Pakistan ta tsunduma cikin rikicin tattalin arziki da siyasa, inda Khan ya matsa wa gwamnatin hadin gwiwa da ke fafutuka don a gudanar da zabe da wuri.

A wani gangamin da aka yi a karshen mako a birnin Lahore, Khan ya maimaita zargin cewa wani babban jami’in leken asiri Manjo-Janar Faisal Naseer na da hannu a wani yunkuri da aka yi na kashe shi a shekarar da ta gabata inda aka harbe shi a kafa.

A cikin wata sanarwa da sashen hulda da jama'a na rundunar soji Pakistan ISPR ya fitar ta bayyana cewa, "wadannan zarge-zarge sun wuce kima kuma abin takaici ne matuka sannan ba za a amince da su ba".

"Hakan dai ya kasance abun da aka saba yi tun shekarar da ta gabata inda ake yawan kai wa jami'an soji da na leken asiri hari da zarge-zarge da farfaganda masu tsauri don ci gaban manufofin siyasa," in ji sanarwar.

TRT Afrika da abokan hulda