An soke ziyarar da Firaiministan Czech zai kai Nijeriya saboda 'ba za a iya daukar dawainiyarsa ba'

An soke ziyarar da Firaiministan Czech zai kai Nijeriya saboda 'ba za a iya daukar dawainiyarsa ba'

Gwamnatin Nijeriya ta soke ziyarar da firaiministan Jamhuriyar Czech Petr Fiala zai kai kasar, tana mai cewa ba za ta iya "daukar dawainiyarsa ba."
Jamhuriyar Czech na cikin kasashen da ke goyon bayan Isra'ila a hare-haren da take ci gaba da kai wa Gaza / Hoto: Reuters

Gwamnatin Nijeriya ta soke ziyarar da Firaiministan Jamhuriyar Czech Petr Fiala da tawagarsa ta 'yan kasuwa za su kai kasar jim kadan kafin ya tafi kasar, tana mai cewa ba za ta iya daukar dawainiyar ziyarar ba.

Sai dai kafofin watsa labaran Jamhuriyar Czech sun rawaito cewa matakin nan gwamnatin Nijeriya, wanda ta dauka kwana kafin isar Fiala da tawagarsa ta kasuwanci kasar, na da alaka da goyon bayan da Czech take bai wa Isra'ila.

Gwmnatin Nijeriya ta shaida wa tawagar firaiministan cewa ba za ta iya daukar dawainiyar ziyarar Fiala da tawagarsa ba.

Hakan ne ya sa aka soke ziyarar, a cewar kakakin gwamnatin Jamhuriyar Czech Vaclav Smolka a hirarsa da manema labarai a Nairobi, babban birnin Kenya, inda suka je bayan ziyarar da suka kai Ethiopia, a cewar kafar watsa labarai ta Irozhlas.

Ziyarar kwana biyu

An tsara cewa firaiministan da tawagarsa za su isa Nijeriya ranar Talata domin yin ziyarar aiki ta kwana biyu.

Sai dai kafar watsa labarai ta Irozhlas ta ambato wasu majiyoyin diflomasiyya suna cewa matakin na Nijeriya na da nasaba da matsayin Jamhuriyar Czech na goyon bayan Isra'ila a hare-haren da take ci gaba da kai wa Falasdinawa.

Ta kara da cewa Jamhuriar Czech, tare da Amurka da Isra'ila, na cikin kasashe 14 da suka yi fatali da kudurin Majalisar Dinkin Duniya na tsagaita wuta a Gaza ranar 27 ga watan Oktoba.

Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da dubu doma, ciki har da kananan yara 4,237 da mata 2,719 tun lokacin da ta kaddamar da hare-hare a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar alkaluman baya-bayan nan na Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta kasar.

AA