Wani mai magana da yawun yan sanda a Pakistan ya tabbatar da cewa wadanda suka tsira daga harin ƴan Japan ne kuma a halin da ake ciki suna karkashin kulawar jami'an. / Hoto: Reuters  

Ƴan sanda a birnin Karachi da ke yankin kudancin Pakistan sun harbe wani ɗan ƙunar baƙin wake da kuma wasu ƴan bindiga a lokacin da suke ƙoƙarin kai hari kan wata mota mai ɗauke da wasu ƴan kasar Japan biyar, waɗanda dukkansu suka tsira, a cewar mai magana da yawun ƴan sandan.

Ƴan bindigan waɗanda ke neman hamɓarar da gwamnati tare da kafa tsarin mulkinsu mai tsauri, sun ƙaddamar da wasu hare-hare mafi muni a Pakistan cikin ƴan shekarun da suka gabata, inda a wasu lokutan sukan kai hari kan ƴan kasashen waje, kamar ƴan China.

Waɗanda suka tsira daga harin ƴan Japan ne kuma a halin da ake ciki suna ƙarƙashin kulawar jami'an, a cewar mai magana da yawun ƴan sandan, Abrar Hussain Baloch, a ranar Juma’a.

Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.

TRT World