'Yan sandan sun ce sun kuma yi nasarar kubutar da mutum 35 da aka yi garkuwa da su da kuma gano wasu ababen hawa guda bakwai da aka sace.

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta kama wasu mutum tara wadanda take zargi da aikata tsafi, da wasu mutum 92 da ake zargin ’yan fashi da makami ne da kuma wasu mutum 153 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne don neman kudin fansa.

Sannan rundunar ta ce ta yi nasarar kuɓutar da mutum 35 da aka yi garkuwa da su da kuma gano wasu ababen hawa bakwai da aka sace.

Kazalika farmakin ya gano wasu makamai 44 da harsasai 447, kamar yadda wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X ta bayyana a ranar Laraba.

An samu wannan nasara ce a wani farmaki da rundunar ta kai bayan samun wasu bayanan sirri kan wasu gungun masu aikata laifuka da suke safarar bindigogi a kan iyakokin kasashe wadanda suke aiki a cikin jihar Filato.

Sanarwar ta ce gungun ne ke samar da bindigogi da harsasai ga masu aikata miyagun laifuka.

Sannan ’yan sandan sun yi nasarar kama mutum goma da ake zargi ciki har da wani babban mai safarar makamai a Karamar Hukumar Obudu a Jihar Cross River, wanda yake samar wa ’yan aware da sauran masu aikata miyagun laifuka makamai a wasu kasashe masu maƙwabtaka da Nijeriya.

Kazalika rundunar ta kama wasu gungun mutane da suke safarar makamai da satar mutane a garin Sutai a Karamar Hukumar Bali a Jihar Taraba, kuma yayin farmakin an yi nasarar kama mutum biyu da ake zargi.

Sanarwar ta ce mutanen biyu suna cikin gungun da suka ƙware wajen satar shanu da safarar bindigogi.

Rundunar musamman ta ’yan sanda a Abuja ta yi nasarar kama wani da ake zargi daga ƙauyen Audi, wanda ya amsa cewa yana cikin gungun masu garkuwa da mutane da masu samo musu bayanai.

An gano wurin da ake ƙera bindigogi a jihar Filato

Rundunar ƴan sandan Nijeriya a Jihar Filato ta ce ta gano wani wuri da ake ƙera bindigogi na gida a garin Kuru kusa da Jos, bayan wani farmaki da rundunar ta kai wurin.

An gano bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu da ƙananan bindigogi masu sarrafa kansu guda tara da kuma harsasai 1,800.

A baya-bayan nan Jihar Filato ta yi fama da rikice-rikice masu nasaba da addini da kuma ƙabilanci wadanda suka yi sanadin asarar rayuka da dama da kuma lalata dukiya mai yawa.