Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare yankin Gaza. / Photo: AFP

1405 GMT –– An lalata mutuncin bil'adama a Gaza - Ministan Turkiyya

Ministan Lafiya na Turkiyya ya ce ana lalata mutuncin bil'adama a Gaza a yayin da ake ci gaba da kai hare-hare ba kan fararen hula ba har ma da cibiyoyin kiwon lafiya.

A wani taron Majalisar Lafiya ta Duniya (WHA) a Geneva, Fahrettin Koca ya ce "A Gaza, ana lalata mutuncin bil'adama a gaban dukkan idanunmu, ana yi mata rugu-rugu."

"An ga cewa kasashen da ke ikirarin ci gaba su ne a baya sosai a fannin darajta dan'adam, sun gwammace su yi shiru yayin da ake kashe yara da jarirai da hanyoyin a salon da ake tunanin ya gushe a duniya," in ji shi. Ya kara da cewa: "Wadanda ake kiran sun fi kowa ci gaba a fannin dimokuradiyya su ne masu ƙin mayar da hankali kan kukan al’umma”.

"Dukkanmu mun kasance fursunonin wannan baƙin tarihi" ya ce.

1233 GMT –– Sifaniya, Ireland da Norway sun amince da ƙasar Falasɗinu a hukumance

Ƙasashen Sifaniya da Norway da Ireland a hukumance sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa, inda suka yi watsi da Isra'ila wadda ta yi Allah wadai da matakin.

Ƙasashen uku na Turai na ganin cewa wannan matakin na su na da tasiri matuƙa kuma zai jawo wasu ƙasashen su amince da Falasɗinun a matsayin ƙasa.

A daidai lokacin da Norway ta amince da ƙasar, Ministan Harkokin Waje Espen Barth Eide ya jinjina dangane da wannan matakin.

1107 GMT –– Isra'ila ta jefa ƙarin bama-bamai a Rafah

Isra’ila ta sake tayar da bam a Rafah da ke kudancin Gaza duk da ƙasashen duniya sun nuna ɓacin ransu dangane da wani hari da Isra’ilar ta kai da ya ƙona tantuna a sansanin gudun hijira na birnin inda har mutum 45 suka rasu.

Harin wanda likitocin Gaza suka bayyana cewa ya jikkata fararen hula da dama, ya jawo Allah wadai daga ƙasashen duniya da shugabannin duniya, inda aka yi niyyar tattaunawa kan lamarin a taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Irin mummunan kisan da aka yi, ƙonannun gawawwakin yara da mata da aka kai su Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya jawo Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Gutteres ya sanar da cewa “babu wani amintaccen wuri a Gaza. Akwai buƙatar a dakatar da wannan abin tsoron.”

0500 GMT –– Sifaniya, Ireland da Norway za su amince da ƙasar Falasɗinu a hukumance

Sifaniya, Ireland da Norway za su amince da ƙasar Falasɗinu a hukumance a yau duk kuwa da fushn da Isra'ila take yi, inda aka mayar da ita saniyar-ware sakamakon luguden wuta da ta kwashe watanni bakwai tana yi a Gaza.

Ƙasashe 144 cikin 193 mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya sun amince da Ƙasar Falasɗinu, cikinsu har da Turkiyya, Rasha, China da India.

Mahukunta a biranen Madrid, Dublin da Oslo sun ce sun ɗauki matakin amince da Ƙasar Falasɗinu ne a wani yunƙuri na gaggauta hana Isra'ila ci gaba da kai hare-hare a Gaza.

Duk da yake matakin da ƙasashen za su ɗauka na je-ka-na-yi-ka ne, ammasuna fata hakan zai sa sauran ƙasashen Turai su bi sahunsu.

2126 GMT —Kwamitin Tsaro na MDD zai yi taron gaggawa bayan Isra'ila ta yi kisan kiyashi a Rafah

Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya zai gudanar da taron gaggawa bayan wani hari da gangan da Isra'ila ta kai sansanin Falasɗinawa 'yan gudun hijira a birni Rafah da ke kudancin Gaza, lamarin da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 45 kana ya jikkata fiye da mutum 250.

Wasu daga cikin mutanen an kashe su ne ta hanya yin gunduwa-gunduwa da su, yayin da aka ƙona wasu.

Ƙasar Aljeriya ce ta buƙaci a yi taron gaggawar, ko da yake ita wakiliyar dindindin ba ce ta majalisar.

Isra'ila ta kashe mutanen na Rafah ne ta hanyar yin gunduwa-gunduwa da su, yayin da ta ƙona wasu./Hoto: AA

2017 GMT — Sakatare Janar na MDD ya soki Isra'ila kan harin da ta kai Rafah Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi tir da Isra'ila kan harin da ta kai yankin Rafah da ke kudancin Gaza, yana mai cewa harin ya yi sanadin "mutuwar fararen-hula da ba su da laifi waɗanda ke samun mafaka daga munanan hare-haren da ake kai wa."

"Babu wani tudun-mun-tsira a Gaza. Dole a daina wannan bala'i," in ji Guterres a saƙon da ya wallafa a soshiyal midiya.

TRT Afrika da abokan hulda