An kashe sojojin Isra'ila uku a yakin da ake yi a arewacin Gaza / Hoto: Reuters

Friday, October 25, 2024

1348 GMT — Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe sojojinta uku a wani fada da aka gwabza a arewacin Gaza yayin da take ci gaba da kai wani gagarumin farmaki a yankin.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce sojojin sun "fadi mutu ne a lokacin da ake gwabza fada a arewacin Gaza", wanda ya kawo adadin sojojin Isra'ila da aka kashe a yakin Gaza zuwa 361 tun bayan fara kai farmakin kasa a yankin a bara.

1319 GMT — Harin da Isra'ila ta kai kan fararen hula a Gaza ya kashe Falasdinawa tara

Akalla Falasdinawa 9 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan wasu fararen hula a yammacin birnin Gaza.

Wata majiyar lafiya daga asibitin al-Ahli Arab ta shaida wa Anadolu cewa an kai wadanda suka jikkata da dama cibiyar lafiyar da kuma gawarwakin mutane tara bayan harin saman.

An kai harin ne a sansanin 'yan gudun hijira na Shati, kamar yadda shaidu suka shaida wa Anadolu.

1439 GMT —

Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce mutane biyu sun mutu a wani harin da aka kai a wani gari a arewacin Isra'ila

Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce mutane biyu ne suka mutu a wani hari da aka kai kan Majd al Krum a arewacin Isra'ila, bayan wata sanarwar da kungiyar Hezbollah ta fitar ta ce ta kai hari kan garin Karmiel da ke arewacin Isra'ila da wani babban makami mai linzami.

1436 GMT — Kungiyar Hezbollah ta kai hari kan tankar Isra'ila ta Merkava a kudancin Lebanon

Kungiyar Hezbollah ta ce ta kai hari kan wata tankar yaki ta Merkava na Isra'ila a wajen garin Marwahin da ke kudancin kasar Lebanon, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani ma'aikacin jirgin tare da jikkata wani.

Kazalika tankar ta kama da wuta bayan da harin makami mai linzami ya same ta.

Kungiyar ta kuma ta harba rokoki a yankin Karmiel a arewacin Isra'ila.

TRT World