Wannan dai shi ne hari na biyu na ‘yan bindiga da aka sanar a cikin sa’o’i 24 a arewa maso yammacin Pakistan. / Hoto: AFP

Akalla mutane 28 da suka haɗa da fararen hula biyar da sojoji 10 da kuma wasu da ake zargin 'yan bindiga 13 ne aka kashe a hare-haren da aka kai a arewa maso yammacin Pakistan cikin sa'o'i 24 da suka gabata, a cewar wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar.

Wani harin da aka kai a wani sansanin soji da ke arewa maso yammacin Pakistan a ranar Litinin ya kashe jami’an tsaro takwas, kamar yadda rundunar sojin ta sanar a ranar Talata, bayan da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da wata mota dauke da bama-bamai a jikin wata katanga.

Jami'an tsaro sun kashe dukkan maharan guda 10 da ke da hannu a lamarin, kamar yadda wata sanarwa da rundunar ta fitar ta faɗa.

Daga cikin wadanda suka mutu a harin na ranar Litinin har da sojoji bakwai da sojan sa-kai guda daya.

Wani hari na biyu da aka kai ranar Talata a wata cibiyar kiwon lafiya a arewa maso yammacin Pakistan ya kashe mutane bakwai da suka hada da ma'aikatan kiwon lafiya da yara da sojoji, in ji rundunar sojin kasar a ranar Talata.

An kashe dukkan mayaƙan sa kan uku a wani harin mayar da martanin da dakarun tsaro suka yi, in ji sanarwar.

Wannan dai shi ne hari na biyu na ‘yan bindiga da aka sanar a cikin sa’o’i 24 a arewa maso yammacin Pakistan.

TRT World