Rahotanni daga ƙasar Saudiyya na cewa an ga jinjirin watan Ramadana a ƙasar.
Shafin Haramain Sharifain ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafukansa na sada zumunta.
Za a soma azumin ne a gobe Litinin, 11 ga watan Maris ɗin 2024, wanda ya zo daidai da 1 ga watan Ramadana shekarar ta 1445 bayan Hijira.
Tun da farko dai an rinƙa samun cikas wurin ganin watan a sassa daban-daban na Saudiyya sakamakon hazo da kuma ƙura wanda har aka soma cire rai daga ganin watan. Sai dai daga baya an tabbatar da ganin watan a ƙasar.
Ƙasashen duniya irin su Philippines, tuni suka yi sanarwa kan cewa ba su ga watan na Ramadana ba inda suka ce sai ranar Talata, 12 ga watan Maris za su tashi da azumi.
Dama a kowace shekara ana soma duba watan na Ramadana ne a ranar 29 ga watan Sha'aban, idan an ga watan akan tashi da azumi washe gari, amma idan ba a gani ba, akan cike watan na Sha'aban kwana 30 sai a tashi da azumi ranar ɗaya ga watan Ramadana.