Yarjejeniyar tsagaita wutar ta fuskanci zazzafar turjiya daga abokan gamayyar Netanyahu masu tsattsauran ra’ayi, waɗanda da goyon bayansu ne Netanyahu ya dogara wajen ci-gaba da mulki. / Hoto: Reuters

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce an cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma musayar fursunonin da ake tsare da su a Gaza da aka yi wa ƙawanya a yankin Falasɗinawa.

Sanarwar ta ranar Juma’a ta zo ne kwana guda bayan ofishin Netanyahu ya ce an samu matsala a tattaunawar da ake yi ta ‘yantar da fursunonin da aka yi garkuwa da su da tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin fursunonin Falasɗinawa.

Netanyahu ya ce zai kira taron majalisarsa ta tsaro daga nan kuma gwamnati za ta amince da yarjejeniyar.

Da alama sanarwar ta Netanyahu za ta share fagen amincewar gwamnatin Isra'ila da yarjejeniyar, wadda za ta dakatar da yaƙin da ta ke yi na kisan ƙare dangi a Gaza da kuma ganin an sako fursunonin Falasdinawa da Isra'ila ta kama.

Haka kuma za ta bai wa dubban ɗaruruwan Falasɗinawa da suka rasa matsugunnansu damar komawa abin da ya yi saura na gidajensu da aka yi wa ruwan bama-bamai a Gaza.

Duk da sanarwar tsagaita wuta da Isra'ila ta yi, ta kashe Falasɗinawa aƙalla 90 a ranar Alhamis a yankin da yaƙi ya ɗaiɗaita.

A yaƙin da ta ke yi na kisan ƙare dangi a Gaza - da a yanzu yake cikin kwana na 469 - Isra'ila ta kashe Falasɗinawa kimanin 46,800 tare da raunata wasu 110,453.

Bincike ya nuna ƙiyasin da Falasɗinawa suke yi na yawan mutanen da aka kashe bai kai ainihin waɗanda suka rasa rayukansu a yaƙin ba, waɗanda adadinsu zai iya kaiwa kimanin 200,000.

A cewar mujallar lafiya ta The Lancet, kimanin mutane 186,000 ne suka mutu tun lokacin da Isra'ila ta fara mamaye Gaza a watan Oktoban 2023. Lancet kuma ta yi ƙiyasin cewa adadin waɗanda suka mutu sakamakon harin da sojojin Isra'ila suka kai a Gaza zuwa Yuni 2024, ya kai 64,260, ƙarin fiye da kashi 41 cikin ɗari na alƙaluman da jami'an lafiyar Falasɗinu suka bayar.

A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutane 4,068 tun daga watan Oktoban 2023.

TRT World