Mohamed Bazoum ya yi korafin cewa sojojin da suka yi masa juyin mulki sun tsare shi a wani wuri sannan suna tilasta masa cin busasshiyar shinkafa da taliya. Hoto: Reuters

Amurka ta ce za ta dora alhakin duk wani abu da ya samu zababben shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum da iyalansa da 'yan majalisar gwamnatinsa da ke tsare, kan sojojin da suka yi juyin mulki a kasar.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, bayan da a hannu guda shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ma suka yi nasu taron kan batun juyin mulkin.

Amurka ta bi sahun Kungiyar ECOWAS wajen yin kira da a mayar da Jamhuriyar Nijar kan turbar kundin tsarin mulki, in ji wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar ta fitar.

Sanarwar na zuwa ne bayan Mohamed Bazoum ya yi korafin cewa sojojin da suka yi masa juyin mulki sun tsare shi a wani wuri sannan suna tilasta masa cin busasshiyar shinkafa da taliya.

A baya-bayan nan ne Amurka ta dakatar da wasu shirye-shirye na jin kai da tallafi da take yi a Nijar bayan da sojoji suka hambarar da zababben shugaban kasar.

Amurka ta kuma yaba da matsayar da ECOWAS ta cimma a karshen taronta na ranar Alhamis inda ta umarci dakarunta su sanya damarar yaki da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar din.

"Amurka ta ji dadin jajircewar ECOWAS na amfani da daukar kowane irin mataki don warware rikicin da dawo da zaman lafiya a kasar," in ji Blinken.

Shugaban MDD ma ya damu da 'mawuyacin halin' da Bazoum ke ciki

Shi ma Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a ranar Laraba ya bayyana matukar damuwa game da "mawuyacin halin" da shugaban Nijar Mohamed Bazoum da iyalansa ke ciki sakamakon tsarewar da sojoji suke yi musu.

"Sakatare Janar yana jaddada damuwarsa game da koshin lafiya da tsaron shugaban kasa da iyalansa kuma yana kara kira da a sake shi nan take ba tare da wasu sharudda ba kuma a mayar da shi kujerarsa ta shugaban kasa," a cewar sanarwar da kakakin Guterres ya fitar.

Reuters