Amurka ta rufe ofishin jakadancinta a Tanzania na tsawon kwanaki biyu saboda katsewar internet da ta shafi kasashen Gabashin Afirka da dama.
"Saboda munanar hanyoyin sadarwa a kasa baki daya, za a rufe ofishin jakadancin daga jama'a," in ji wata sanarwa da ofishin ya fitar ta shafin X.
Tanzania ce kasar da ta fi illatuwa a yankin saboda katsewar yanar gizon da matsalolin wayoyin sadarwa na karkashin teku suka samu a ranar Lahadi.
Ofishin jakadancin ya bayyana cewa bangaren harkokin bayar da visa zai zama a kulle a ranakun Talata da Laraba, wadanda suka shirya zuwa sai su jira sanarwar wani lokaci a nan gaba.
Bukatun gaggawa
Za a bude bangaren harkokin visa don karba da kuma bukatar gaggawa ga 'yan kasar Amurka, in ji sanarwar.
Ofishin jakadancin da ke garin Dar es Salaam na gabar teku na daya daga manyan cibiyoyin diplomasiyya a kasar.
OtheSauran kasashen da matsalar ta shafa sun hada da kenya, rwanda da Uganda, inda Mozambique da Malawi kuma suka sukanta kadan.
Irin wannan matsala ta afku a wasu kasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka a watan da ya gabata wanda aka dora alhakinta kan matsalar da wayoyin sadarwa na karkashin teku suka samu.