Jirgin saman yakin Amurka samfurin RAF Typhoon daga RAF Akrotir a yayin da yake kan hanyar kaddamar da hare-hare / Hoto: Reuters

Sojojin Amurka da na Birtaniya sun kai hare-hare a yankunan 'yan tawayen Houthi na Yemen, inda suka yi amfani da jiragen ruwan yaki wurin harba makamai masu linzami samfuran Tomahawk tare da jiragen sama na yaki.

Sojojin sun kai hare-hare a wuraren da suka hada da ma'ajiyar makamai da na'urorin kare hare-hare ta sama, a cewar jami'an gwamnatin Amurka ranar Juma'a da safe.

Wadannan hare-hare su ne karon farko da Amurka ta yi martani kan 'yan tawayen Houthis wadanda suka dade suna yin amfani da jirage marasa matuka da makamai masu linzami wajen kai hari kan jiragen ruwa na daukar kaya da ke zuwa Isra'ila tun lokacin da aka kaddamar da hare-hare a Gaza.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce hare-haren da suka kai Yemen sun nuna cewa kasarsa da kawayenta ba za su "lamunci" hare-haren da 'yan tawayen Houthi suke kai wa jiragen ruwansu ba.

A wata sanarwa da ya fitar, Biden ya ce a karon farko sun yi amfani da makamai masu linzami na ruwa wajen kai hare-hare kan 'yan tawayen Houthi domin yin raddi game da jerin hare-haren da suke kai wa jiragen ruwa da ke wucewa ta Bahar Maliya.

A gefe guda, shugaban Houthi Ali al-Qahoum ya ce sun kaddamar da hare-hare kan jiragen yakin Amurka da Birtaniya da ke Bahar Maliya domin yin martani kan hare-haren da aka kai musu.

"Amurkawa da Masu kishin Yahudawa da Birtaniya da ke yaki da Yemen sun kaddamar da jerin hare-hare a babban birnin, Sanaa, da yankin Hudaida da Saada, da kuma Dhamar," a cewar wani jami'in Houthi Abdul Qader al Mortada a sakon da ya wallafa a shafin X.

Wakilan kamfanin dillancin labarai na Associated Press journalists a Sanaa sun ce sun ji kara hudu ta fashewar wasu abbuwa amma ba su ga alamar jiragen yaki ba.

Mutum biyu mazauna Hudaida, Amin Ali Saleh da Hani Ahmed, sun ce sun ji kara guda biyar ta fashewar bama-bamai. Hudaida yanki ne da ke tsakanin Bahar Maliya kuma shi ne birni mafi girma mai tashar jiragen ruwa da ke karkashin Houthis.

TRT World