Algeria, China, Russia blast Israel at UNSC over Haniyeh assassination

Wakilan Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNSC) sun yi Allah wadai da kisan gillar da Isra'ila ta yi wa shugaban ƙungiyar Hamas Ismail Haniyeh a Tehran babban birnin Iran, yayin da wakilan dindindin na Amurka da Birtaniya suka zargi Iran da janyo rashin zaman lafiya a yankin.

A ranar Labara ne Majalisar ta kira wani zaman gaggawa kan kisan gillar da aka yi wa Haniyeh bisa buƙatar Iran inda ƙasashen Rasha da Aljeriya da kuma China suka yi maraba da hakan.

Da yake jawabi a wajen taron, jakadan China Fu Cong ya ce, ƙasarsa ta yi kakkausar suka ga kisan gillar da aka yi wa Haniyeh.

Kazalika wakilin Aljeriya a MDD Amar Bendjama ya ce: "Muna kan hanyar zuwa ga bala'i," yana mai cewa harin Isra'ila wani "ta'addanci ne" wanda ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma iko da 'yancin Iran.

''Wannan ba wai hari ne kan mutum ɗaya ba, ƙazamin hari ne kan tushen dangantakar diflomasiyya da take ikon ƙasa da kuma ƙa'idojin da ke ingiza tsarinmu na duniya, '' in ji shi.

'A ina wannan hauka za ta ƙare?'

Bendjama ya yi kakkausar suka ga "ta'addancin da haramtacciyar ƙasar Isra'ila ta aikata."

Idan aka ce “Manufar Isra’ila na cin zarafi da taken tsare-tsaren duniya” na haifar da “guguwar tashin hankali da ta mamaye Gaza da Yammacin Kogin Jordan da Yemen da Lebanon da Syria da kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran,” yana mai cewa: “A ina wannan haukar za ta ƙare?

Ya kuma yi kira ga ƙasashen duniya da kar da su yi shiru '' yayin da ake zubar da jinin waɗanda ba su ji ba, ba su kuma gani ba, sannan ana take dokoƙin ƙasa da ƙasa."

Ya ƙara da cewa, ''cikin gaggawa muna kira da a gaggauta tsagaita wuta a Gaza ba tare da wani ɗage haramtacciyar ƙawanyar Isra'ila a can.''

Da yake mara wa Algeria baya, mataimakin wakilin dindindin na Rasha na farko a Majalisar Ɗinkin Duniya Dmitry Polyansky, ya jadadda matsayar ƙasarsa ta Allah wadai da kisan Haniyeh da Isra'ila ta yi, inda ya ƙara da cewa sakamakon harin na da matukar haɗari ga ɗaukacin yankin.

''Ba ƙaramin koma-baya ba ne ga irin tsayin ɗaka da kuma shawarwari kan sulhu tsakanin Hamas da Isra'ila kan batun tsagaita wuta a Gaza, kuma Ismail Haniyeh ya kasance wanda ya ke kan gaba a lamarin. Dole ne dukka mu fahimci hakan,'' in ji Polyansky.

Wakilin na Rasha ya ce harin wani yunƙuri ne na janyo Iran cikin "Yanayin da yankin ke ciki ya rigaya ya yi zafi," yana mai ƙari da cewa, "mummunan al'adar kisan gilla da ake yi wa manyan jami'an siyasa da na soji na ƙara jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin gagarumin yaki a yankin baki ɗaya.''

Ƙudurin kwamitin ya buƙaci a dakatar da farmaki tsakanin Isra'ila da Hezbollah tare da janyewar sojojin Isra'ila daga ƙasar Lebanon da kuma dakarun Lebanon da na UNIFL da aka tura zuwa kudancin Lebanon.

Ƙudurin kwamitin ya buƙaci a dakatar da kai farmakin da ke tsakanin Isra'ila da Hizbullah, da janyewar sojojin Isra'ila daga ƙasar Lebanon da dakarun Lebanon da na UNIFIL da aka tura zuwa kudancin ƙasar Lebanon, da kuma kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke dauke da makamai ciki har da ƙungiyar Hezbollah.

Amurka da Birtaniya sun ɗora wa Iran laifi

Mataimakin wakilin Amurka na dindindin a MDD Robert Wood ya shaida wa majalisar cewa '' Isra'ila ta na da 'yancin kare kanta daga hare-haren Hezbollah da sauran 'yan ta'adda.''

Wood ya jaddada cewa dole ne Iran ta mutunta ƙudurorin kwamitin sulhun, sannan kuma ya kamata majalisar ta yi la'akari da karin matakan da suka ɗauka kan ayyukan Iran da ke barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin. Ya kuma ƙra da cewa Amurka ba ta da wani alaƙa da mutuwar Haniyeh.

''Babu wanda zai tabbatar da cewa za a yi yaki ko kuma ba za yi ba,'' in ji Wood, tana mai ƙari da cewa Iran da ''sauran yan ta'adda" da take tallafawa a kullum suna haifar da ƙara rura barazanar rikici a yankin.''

Jakadiyar Burtaniya Barbara Woodward ta kuma jaddada cewa yawan tashe-tashen hankula ba son kowa ba ne. Tana mai ƙira kan zaman lafiya da kuma gaggauta dakatar da hare-hare, wanda a cewar Wood "Ba za a taba samun zaman lafiya na tsawon lokaci ta hanyar bama-bamai da harsasai ba."

Wood ta bayyana cewa, ƙungiyar Houthi na ci gaba da kai hare-hare kan Isra'ila inda ta ce dole ne a kawo ƙarshen hakan.

Kazalika ta jaddada aniyar Birtaniya na tabbatar da tsaro ga Isra'ila, tana mai cewa Isra'ila na da 'yancin kare kanta.

AA