Saudiyya ce ƙasar da ta fi sayen makamai daga Amurka. / Hoto: Reuters

Ana sa ran Amurka za ta cire haramcin da ta saka kan Saudiyya dangane da siyar mata da muggan makamai a makwanni masu zuwa, kamar yadda jaridar Financial Times ta bayyana a ranar Lahadi, inda ta ambato wani mai masaniya kan lamarin.

Jim kaɗan bayan ya zama shugaban ƙasa a 2021, Joe Biden ya ɗauki matakai masu tsauri kan Saudiyya musamman dangane da yaƙin ta take yi da mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran waɗanda ke Yemen, inda ake zargin ta yi amfani da makaman domin kashe farar hula da dama.

Saudi Arabia, wadda ita ce ƙasa mafi girma da ke yi wa Amurka cinikin makamai, ta koka dangane da wannan haramcin, wanda ya dakatar da siyar mata da nau’in makaman da gwamnatin baya ta rinƙa siyar mata.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a ranar Laraba ya ce Amurka da Saudiyya na daf da kulla wasu yarjejeniyoyin hadin gwiwa kan makamashin nukiliya da tsaro da da ɓangaren da ya shafi daidaita dangantaka tsakanin Riyadh da Isra'ila.

Sai dai kuma, ɗage haramcin siyar da muggan makamai ba shi da alaƙa kai tsaye da wannan tattaunawar, in ji jaridar ta Financial Times.

Haka kuma Fadar White House da Sashen Watsa Labarai na Gwamnatin Saudiyya ba su ce komai ba dangane da buƙatar da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya aike musu ba dangane da tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamari.

Reuters