Afirka ta Kudu ta shigar da ƙara a Kotun Duniya inda take zargin Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Gaza. / Hoto: Reuters

Afrika ta Kudu ta buƙaci babbar kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙara matsin lamba ga Isra’ila domin ta dakatar da hare-haren da take kaiwa a birnin Rafah da ke kudancin Gaza.

Tuni Pretoria ta gabatar da kokenta dangane da Isra’ila a Babbar Kotun Duniya (ICJ) da ke Hague, inda take zargin hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a Gaza laifukan yaƙi ne.

Har yanzu kotun ba ta yanke hukunci kan lamarin ba, amma a ranar 26 ga watan Janairu, ta bayar da umarni ga Isra’ila da ta tabbatar da kare fararen hula daga cutuwa da kuma barin kayan agaji shiga.

Sai dai duk da haka Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare haka kuma dakarun ƙasar na kai hare-hare a Rafah, inda rabin jama’ar Gaza mai mutum miliyan 2.4 suke neman mafaka sakamakon hare-haren na Isra’ila.

Ƙara ɗaukar mataki

Ga Afirka ta Kudu, tana ganin wannan ya isa Kotun Duniya ta sake waiwayar umarnin da ta bayar da kuma ƙara jan kunne.

A ranar Talata ƙasar ta bayyana cewa “ta damu matuƙa kan hare-haren da Isra’ila ta sanar tana kaiwa a Rafah wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, da cutarwa da lalata wurare,” in ji ƙasar.

Kotun ba ta tabbatar da samun buƙatar Afirka ta Kudu ba, kuma ba lallai ne ta yi la'akari da buƙatar ba.

AFP